Yanzu Yanzu: Najeriya za ta siyi helikoftan kai hari 12 daga Rasha bayan yarjejeniyar soji

Yanzu Yanzu: Najeriya za ta siyi helikoftan kai hari 12 daga Rasha bayan yarjejeniyar soji

Kasar Rasha za ta siyarwa Najeriya helikoftan kai hari 12 bayan kasashen biyu sun shiga wata yarjejeniyar soji a gefen taron Rasha-Afrika wanda ke gudana a Sochi.

Reuters, da take kawo wani rahoto daga kamfanin dillancin labaran Moscow RIA, ta ayyana cewa an kulla yarjejeniyar ne a ranar Alhamis, 24 ga watan Oktoba a Sochi.

Da farko, hadimin shugaban kasa, Garba Shehu, ya bayyana cewa Shugaba Buhari zai tattauna da Shugaba Vladimir Putin na Rasha, wanda daga ciki zai danganci siyan makamai.

Gabannin taron na Rasha da Afrika, Legit.ng ta rahoto ewa kasar Rasha na iya taimakawa Najeriya wajen yaki da yan ta'adda Boko Haram idan kasashen biyu suka kulla wata yarjejeniya ta fasahar soji wanda aka shirya gudanarwa a Oktoba 2019.

Jakadan Najeriya a Rasha, Steve Ugbah, ya fada ma kamfanin dillancin labaran Rasha RIA a wani hira cewa shugaba Buhari ya shirya ganawa da Shugaba Putin a gefen taron Rasha da Afrika a birnin Black Sea na Sochi.

KU KARANTA KUMA: Sanatan Kaduna ya sha alwashin fallasa karin cibiyoyin horar da kangararru da basa bisa ka’ida

Ugbah yace an riga an shirya yarjejeniya tsakanin Rasha da Najeriya gabannin haduwar shugabannin biyu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel