Wata sabuwa: Za'a karrama zakin da ya kufce daga gidan Zoo na Kano

Wata sabuwa: Za'a karrama zakin da ya kufce daga gidan Zoo na Kano

- Wata kungiyar kare hakkin dan adam ta jihar Kano ta sha alwashin karrama katon zakin nan da ya kufce daga gidan Zoo na jihar Kano

- Kungiyar ta ce za ta yi wannan biki ne domin ganin yadda zakin ya shafe wuni biyu yana yawo a cikin gari ba tare da ya cutar da mutum ko daya ba

- Kungiyar ta ce nan ba da dadewa ba za ta sanar da ranar da za ta gabatar da wannan shagalin biki

Kungiyar kare hakkin dan adam a jihar Kano ta kammala shiri tsaf domin shirya wani kasaitaccen biki na karramawa ga wannan katon Zakin da ya kuce daga gidan Zoo na jihar Kano a karshen makon da ya gabata.

SHugaban kungiyar Qaribullahi Yahya Lawal Kabara ya sanar da cewa za su yiwa zakin wata gagarumar kyauta sakamakon yadda ya shafe tsawon wuni biyu amma bai taba lafiyar dan adam ko guda daya ba, sai ma kare ran mutane da zakin yayi ta hanyar kin cutar da koda jariri.

Duk da cewa dai fitowar zakin daga kejin na shi yayi sanadiyyar rasa rayukan wasu dabbobi a jihar, amma yayi kokari matuka da bai taba lafiyar dan adam ko daya ba, saboda haka kungiyar ta ce ya zama tilas ta karrama wannan zakin.

KU KARANTA: Hotuna: Wata mata ta bayyana yadda saurayinta ya dinga yin luwadi da danta a duk lokacin da ta fita ta bar su tare a gida

Kungiyar ta bayyana cewa nan ba da dadewa ba za ta sanar da ranar da za ta yi wannan shagalin biki na karrama zakin.

Idan ba a manta ba a makon da ya gabata ne wani murgujejen zaki ya kwace daga cikin kejin shi ya fito cikin gari daga gidan Zoo din jihar Kano.

Fitowar zakin ya tada hankalin al'umma inda mutane suka yi ta guje-guje suna neman mafaka, sai dai kuma har zakin ya kammala yawon shi bai cutar da mutum ko daya ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel