Kotu ta daure wani mutum a gidan yari bayan ya yiwa yara 2 fyade

Kotu ta daure wani mutum a gidan yari bayan ya yiwa yara 2 fyade

Wata kotun Majistare dake Kaduna a ranar Alhamis 24 ga watan Oktoba, 2019 ta bayar da umarnin rufe Yusuf Yahaya mai shekaru 27 a gidan yari bisa aikata laifin sata tare da yiwa yara 2 fyade.

Alkalin kotun, Lukman Sidi ya bada umarnin a tsare Yusuf a gidan yarin ne har zuwa lokacin da za a kammala sauraron shari’ar tasa.

KU KARANTA:El-Rufai ya bai wa al’ummar Kaduna hakuri a kan matsalar tsaro

Sidi ya nemi hukumar ‘yan sanda wadda ta shigar da karar da ta kai rubutaccen bayani game da karar zuwa ka hukumar DPP domin jin ta su shawarar.

Hukumar ‘yan sandan na tuhumar Yusuf ne wanda ke zaune a jihar Kano da laifin satar mutane da kuma fyade. Wadannan laifukan kuwa duk sun ci karo da dokar Penal Code ta jihar Kaduna a sashe na 59, 246 da 258.

Insfekta Chidi Leo wanda shi ne jami’in dan sandan da ya shigar da karar ya ce, Abdullahi Mohammed wanda ke zaune karamar hukumar Kauru ta jihar Kaduna shi ne ya kawo rahoto a ofishinsu ranar 30 ga watan Satumba.

Kamar yadda Abdullahi ya shaidawa hukumar ‘yan sanda, cewa yayi kamar kimanin karfe 11 na dare ne Yusuf ya shiga gidansu ya sace mata biyu daga cikin ahalin gidan.

Bugu da kari, bayan satar ‘yan matan wanda ake karar ya bukaci a biya shi kudi naira miliyan 2 kafin ya sake su. Bayan shiga bincike da hukumar ‘yan sanda tayi aka samu nasarar damke Yusuf Yahaya a inda ya boye, inji Leo.

https://www.dailytrust.com.ng/court-remands-man-for-allegedly-kidnapping-raping-2-teenagers.html

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel