Majalisar wakilai: APC ta sha kaye yayinda dan takarar PDP ya lallasa ta a jihar Kogi

Majalisar wakilai: APC ta sha kaye yayinda dan takarar PDP ya lallasa ta a jihar Kogi

Barista Ibrahim Shabba na majalisar wakilai ya kayar da wani mamba na jam’iyyar All Progressive Congress (APC) a kotun daukaka kara.

Legit.ng ta tattaro cewa dan APC da aka kayar shine Hon. Abdulkarim Usman Isah Wambai mai wakiltan mazabar Lokoja-Kogi Kotonkarfe (KKF).

Injiniya Musa Wada, dan takarar gwamna na PDP a zaben gwamnan jihar Kogi mai zuwa ne ya sanar da nasarar Shabba a wani rubutu da ya wallafa a shafin Twitter.

Wada ya wallafa a twitter a ranar Laraba cewa: “Barka Barista Ibrahim Shabba akan nasararka a kotun daukaka kara a yau. Muna alfahari da kai sannan muna yi maka fatan samun nasara yayinda ka dauki hanyar bauta wa mutanen mazabar Lokoja/Koto masu alkhairi.”

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: Najeriya ta motsa a cikin sahun Kasashen da ke da saukin kasuwanci

A wani labarin kuma mun ji cewa Jam’iyyar Peoples Democratic Party PDP) a ranar Laraba, 23 ga watan Oktoba, ta bayyana cewa za ta fara kamfen dinta na jihar Kogi a lokacin wani biki a Lokoja a ranar Juma’a.

Babban sakataren labaran PDP na kasa, Mista Kola Ologbondiyan, a wani jawabi ya kuma bayyana cewa jam’iyyar ta gano wani makirci da jam’ iyyar All Progressives Congress (APC) da gwamnan jihar, Yahaya Bello ke shiryawa na dakile kamfen din.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel