El-Rufai ya bai wa al’ummar Kaduna hakuri a kan matsalar tsaro

El-Rufai ya bai wa al’ummar Kaduna hakuri a kan matsalar tsaro

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya nemi afuwar al’ummar Kaduna musamman wadanda ke wuraren da matsalar tsaro ta fi kamari a jihar.

El-Rufai ya wallafa jawabin neman afuwar ne a shafinsa na Twitter da misalin karfe 12:17 na ranar Alhamis 24 ga watan Oktoba, 2019.

Gwamnan ya ce: “Muna neman afuwarku game da rashin ‘yan uwa da kuka yi. Muna cike da takaicin dawowar ayyukan ‘yan bindiga a wadansu shiyyoyin jihar Kaduna. Kuma ina so in tabbatar maku da cewa mun shirya daukan tsauraran matakan tsaro domin dakile wannan matsala.”

A wani labarin kuwa za ku ji cewa, Gwamnatin tarayyar Najeriya ta shawarci ‘yan kasar da su rinka neman guraben aiki a kasashen waje.

Ma’aikatar kula da harkokin kasashen wajen Najeriya ce ta fitar da wannan sanarwar ta hanyar kakakinta wato Ferdinand Nwoye.

A cikin sanarwar Ferdinand ya bayyana guraben aiki da a ke neman jama’a da kuma kasashen dake neman ma’aikatan. Haka zalika ya bada shafin yanar gizo domin samun karin bayani.

https://twitter.com/elrufai/status/1187327251022524417

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel