Gwamnatin tarayya ta shawarci ‘yan Najeriya da su rinka neman aiki a kasashen waje

Gwamnatin tarayya ta shawarci ‘yan Najeriya da su rinka neman aiki a kasashen waje

Ma’aikatar kula da harkokin kasashen wajen Najeriya ta yi kira ga ‘yan kasar wadanda suka cika sharuddan da ake nema, da su nemi guraben aiki a cibiyar cigaban kasuwanci ta musulunci dake Casablanca na kasar Morocco.

Kamar yadda cibiyar ta bayar sanarwa, duk wanda ya cika sharuddan kasancewa sabon Darakta janar na hukumar zai aika da takardunsa zuwa ga babban ofishin hukumar dake birnin Jiddah a kasar Saudiya.

KU KARANTA:Gwamnatin Yobe ta farfado da wani katafaren kamfanin dake jihar

Mai magana da yawun bakin ma’aikatar kula da harkokin kasashen wajen Najeriya, Ferdinand Nwonye ne ya bada sanarwar labarin, inda ya ce za a rufe neman gurbin wannan aikin ne a ranar 31 ga watan Oktoba, 2019.

Haka kuma ya yi kira ga wadanda suke sha’awar aikin da su ziyarci shafin yanar gizo kamar haka: https://www.oic-oci.org/vacancies/ domin samun karin bayani.

Har ila yau, ma’aikatar ta sake yin kira ga ‘yan Najeriya da su nemi guraben mukamin jami’in hulda da jama’a wato Public Relations (PR) da kuma mai isar da sako na musamman a ma’aikatar IOFS, dake kasar Kazakhstan. Ga me sha’awa zai iya ziyartar wannan shafin: https://www.oic-iofs.org/ domin karin bayani.

A wani labarin kuwa zaku ji cewa, Gwamna Mai Mala Bunin a jihar Yobe ya farfado da wani katafaren kamfanin sakar buhu a jihar bayan ya kwashi tsawon shekaru takwas bai aiki.

Rahotanni sun tabbatar mana da cewa wannan kamfanin dai shi ne na uku da gwamnatin jihar Yoben ta tayar a halin yanzu. Sauran biyu din kuwa su ne, kamfanin fulawa da kuma kamfanin sarrafa karafunan Aluminium.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel