Da duminsa: An gurfanar da wani tsohon shugaban INEC

Da duminsa: An gurfanar da wani tsohon shugaban INEC

- Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta sake gurfanar da tsohon shugaban hukumar zabe ta kasa

- Ana zargin Farfesan ne da almundahanar wasu kudade har naira biliyan 1.23

- Amma Farfesan ya musanta hakan. A don haka ne mai shari'ar ya dage sauraron karar zuwa 25 ga watan Nuwamba

Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta kara gurfanar da tsohon shugaban hukumar zabe, Farfesa Maurice Iwu akan zarginsa da take da almundahanar naira biliyan 1.23.

Farfesan ya musanta abinda kae zarginsa.

Mai shari’a Nicholas Oweibo ya aminta da belinsa inda ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 25 ga watan Nuwamba, 2019.

KU KARANTA: Kano 9: An ci zarafin daya daga cikin yaran 9 da aka sace

An fara gurfanar da Iwu ne a ranar 8 ga watan Augusta, 2019 kafin mai shari’a Chuka Obiozor ya tafi hutu.

A lokacin, Farfesan ya musanta zargin da ake masa.

An kara gurfanar dashi ne a yau gaban mai shari’a Jastis Oweibo akan wancana zargin inda har ila yau ya musanta.

A wancan lokacin, an bada belin Farfesan ne akan kudi naira biliyan daya tare da tsayayyu guda biyu. Amma an adana shi a gidan gyaran hali dake Ikoyi kafin cikar sharuddan belinsa.

Mai shari’ar ya bukaci tsayayyen na farko da ya zamo mazunin jihar Legas tare da nuna takardun shaidar mallakar kadara a jihar.

Ya kara da umartar tsayayyun da su bayyana shaidar biyan haraji na shekaru uku da asuka gabata a jihar.

Hakazalika, mai shari’ar ya bukaci wanda ake karar da ya mika fasfotinsa na fita kasashen ketare ga kotun tare da umartarsa da ba zai yi tafiya ba har sai kotun ta aminta da hakan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel