An kama wani fasto kan zargin garkuwa da mutum a Nasarawa

An kama wani fasto kan zargin garkuwa da mutum a Nasarawa

Rundunar yan sandan jihar Nasarawa ta kama wani fasto mai suna Yaren Bala Mkparushama, bisa zargin kasancewa da hannu cikin garkuwa da wata mata mai suna Misis Victoria Nandi Timothy.

Rundunar yan sandan ta ce har ila yau mai laifin yana da hannu cikin karban kudin fansar da ya yi sanadiyar sakin matar da aka sace.

Kwamishinan yan sandan jihar, Bola Longe, ya ce: "An kama wanda ake zargin, Fasto Yaren Bala Mkparushama kan kasancewarsa da hannu a gakuwa da wata Misis Victoria Nandi Timothy a Kurmin Tagwaye, karamar hukumar Akwanga da ke jihar."

A cewar shi, yan sandan wadanda suka shiga aiki da taimakon sashin kwararru sun kama fasto Yarren Bala Mkparushama mai shekara 41 da hannu dumu-dumu cikin lamarin.

Mista Longe yace an kubutar da Misis Victoria Nandi Timothy na Kurmin Tagwaye a karamar hukumar Akwanga dake jihar ne a ranar 10 ga watan Oktoba bayan an biya kudi naira dubu dari biyu (N200,000:00).

Yace, reshen tayi nasara ne sakamakon tabbatattun bayanai da ta samu daga hannun masu basira, da kuma sanya idanu kan shiga da fitar mai laifin.

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: Najeriya ta motsa a cikin sahun Kasashen da ke da saukin kasuwanci

Kwamishinan yan sandan ya yabi kokari shirin Operation Puff- Adder da Sufeto Janar na yan sanda ya kafa.

Mista Longe ya bukaci al’umma dasu taimaki reshen da bayanai don kau da laifuffuka a jihar Nasarawa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel