Da dumi-dumi: Najeriya ta motsa a cikin sahun Kasashen da ke da saukin kasuwanci

Da dumi-dumi: Najeriya ta motsa a cikin sahun Kasashen da ke da saukin kasuwanci

- Najeriya ta shiga sahu na 131 a duniya cikin kididdigan bankin duniya na jerin kasashen da keda saukin kasuwanci, wanda hakan ke nufin tayi tsalle 15 daga sahun da take a 2019

- An samu wannan kididdiga ne bayan an harhada tare da kwatanta kamanceceniyar tsarin kasuwanci a kasashe 190 a fadin duniya

- A wani jawabi da ta saki a baya, babban bankin duniya ya ambaci sunan Najeriya a matsayin daya daga cikin manyan kasashe 20 da ke da saukin yin kasuwanci a fadin duniya

Rahoton da ke zuwa mana a yanzu haka ya nuna cewa Najeriya ce a sahu na 131 a duniya cikin kididdigan bankin duniya na jerin kasashen da ke da saukin kasuwanci, wanda hakan ke nufin tayi tsalle 15 daga sahun da take a 2019.

Cibiyar Bretton Wood ce ta bayyana hakan a cikin rahotonta da ta saki a safiyar ranar Alhamis, 24 ga watan Oktoba.

An samu wannan kididdiga ne bayan an harhada tare da kwatanta kamanceceniyar tsarin kasuwanci a kasashe 190 a fadin duniya.

A wani jawabi da ta saki a baya, babban bankin duniya ya ambaci sunan Najeriya a matsayin daya daga cikin manyan kasashe 20 da ke da saukin yin kasuwanci a fadin duniya, rahoton yace Najeriya na daga cikin manyan kasashe 10 a duniya.

KU KARANTA KUMA: PDP za ta fara kamfen a Kogi a ranar Juma’ a, ta yi zargin bankado wani makirci na Yahaya Bello da APC

Baya ga Najeriya, an kuma ambaci sunayen kasashen Saudi Arabia, Jordan, Togo, Bahrain, Tajikistan, Pakistan, Kuwait, China da India cikin manyan kasashe 10 dake da dadin kasuwanci.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel