Daliban da ke sace kamfen 'Yan mata sun shiga hannun hukuma a wata jihar arewa

Daliban da ke sace kamfen 'Yan mata sun shiga hannun hukuma a wata jihar arewa

Rundunar yan sandan jihar Neja ta kama wasu daliban makarantan sakandare na 'Izom Science Secondary School' a karamar hukumar Gurara dake jihar Neja bisa zargin satan kamfe 'yan mata.

Har ila yau an kama wani Mohammed Ali, dan shekara 24 mai sana’ar dinki a yankin Low Cost dake karamar hukumar Lapai a jihar kan laifi irin guda.

Kakakin rundunar yan sandan reshen, DSP Muhamma D-Inna Abubakar yace an kama daliban ne bayan wadanda lamarin ya shafa sun kai korafi.

Yace reshen ta shiga damuwa saboda an sha samun lamari makamancin haka, inda ya kara da cewa bincike ya nuna cewa masu sace-sacen suna da abokan kasuwanci masu siyan yan kamfen.

Kakakin yace daya daga cikin masu laifin, Mohammed Ali, ya ambaci sunan wani Mallam Madaji Yabajeko dake yankin karamar hukumar Agaie a matsayin mai sayan yan-kamfen.

Mohammed ya fada ma manema labarai cewa ya saci yan kamfai uku a lokuta daban-daban a yankuna daban-daban, inda ya kara da cewa yana yunkurin sace wani wandon ne yayin da wata mata ta tara masa jama'a.

Rundunar yan sandan har ila yau ta gurfanar da wani Daniel Timoth Olamide mai shekaru 32 wanda ya shahara wajen kirkiran takardan shaidan kammala karatu na kwalejin Ilimin jihar ga masu siya a kan kudi N14,000.

KU KARANTA KUMA: PDP za ta fara kamfen a Kogi a ranar Juma’ a, ta yi zargin bankado wani makirci na Yahaya Bello da APC

Mai laifin wanda har ila yau ya kammala karatu daga makarantar, yace ya shiga harkan ne tun 2015, inda ya kara da cewa wata matar da yayi ma taimako ce ta tona mishi asiri.

Rundunar har ila yau ta kama masu fashi da makami wadanda ke shiga hijabi don kai hari kan al’umma.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel