Gwamnatin Jigawa za ta kashe N1.5bn don gina masallatai da wasu ayyuka

Gwamnatin Jigawa za ta kashe N1.5bn don gina masallatai da wasu ayyuka

Gwamnatin jihar Jigawa ta ware naira biliyan 1.5 don fara wasu sabbin ayyuka na mazabu da wasu ayyukan da ake gudanarwa a yanzu a mazabu da 'yan majalisar jihar suke aiwatarwa.

Sakataren gwamnatin jihar, (SSG) Abdulkadin Adamu Fanini ne ya bayyana hakan yayin da ya ke jawabi wurin wani taro na farko tsakaninsa da 'yan kwangila a babban birnin jihar, Dutse.

Fanini ya ce an ware naira miliyan 997 don sabbin ayyuka yayin da an kuma ware naira miliyan 500 don karasa ayyukan da aka fara a jihar a 2017 zuwa 2018.

DUBA WANNAN: Da duminsa: FG ta canja wa ma'aikatar sadarwa suna

Ya yi bayanin cewa an ware naira miliyan 50 don ginin masallacin Juma'a a Kafin Hausa yayin da an kuma ware naira miliyan 20 don wasu ayyukan addinin musulunci.

A cewarsa, gwamnatin jihar za ta duba bukatar na 'yan majalisar suka shigar na gina masallatan Juma'a 134, masallatan Juma'a 23 da kuma gyaran masallatan unguwanni 17 da gina fadar hakimin Babura.

Ya ce, "A kalla 'yan kwangila 283 ne suka nuna sha'awar neman a basu kwangila. Duk wanda aka bawa kwangilar ya tabbatar ya kammala cikin lokacin da aka diba masa."

A jawabinsa, wakilin 'yan kwangilar, Mohammad Danburan Garba ya yabawa gwamnatin jihar da ta ba su kwangilar kuma ya yi alkawarin cewa za su kammala ayyukan a lokacin da aka diba musu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel