PDP za ta fara kamfen a Kogi a ranar Juma’ a, ta yi zargin bankado wani makirci na Yahaya Bello da APC

PDP za ta fara kamfen a Kogi a ranar Juma’ a, ta yi zargin bankado wani makirci na Yahaya Bello da APC

- Jam’iyyar Peoples Democratic Party PDP) ta bayyana cewa za ta fara kamfen dinta na zaben gwamnan jihar Kogi a gobe Juma'a

- PDP a wani jawabinta ta kuma yi ikirarin gano wani makirci da jam’ iyyar All Progressives Congress (APC) da gwamnan jihar, Yahaya Bello ke shiryawa na dakile kamfen din

- Kakakin jam'iyyar, Kola Ologbodiyan ya ce mambobin PDP da magoya bayanta sun rigada sun dauki matakai gabannin hakan

Jam’iyyar Peoples Democratic Party PDP) a ranar Laraba, 23 ga watan Oktoba, ta bayyana cewa za ta fara kamfen dinta na jihar Kogi a lokacin wani biki a Lokoja a ranar Juma’a.

Babban sakataren labaran PDP na kasa, Mista Kola Ologbondiyan, a wani jawabi ya kuma bayyana cewa jam’iyyar ta gano wani makirci da jam’ iyyar All Progressives Congress (APC) da gwamnan jihar, Yahaya Bello ke shiryawa na dakile kamfen din.

Sai dai kuma ya ce mambobin PDP da magoya bayanta sun rigada sun dauki matakai gabannin hakan, inda yace a shirye suke su tunkari da hana APC da Bello gudanar da shirinsu.

KU KARANTA KUMA: Gaskiyar dalilin da yasa muke gudanar da kare kasafin kudi cikin sirri – Majalisar wakilai

Kakakin na PDP ya kuma yi ikirarin cewa tuni PDP keda kaso 70 na masu zabe da aka yiwa rijista a kananan hukumomi 18 cikin 20 da ke jihar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel