Achuba: Buhari ya fadawa Yahaya Bello ya shiga taitayinsa – ‘Yan Majalisar hamayya

Achuba: Buhari ya fadawa Yahaya Bello ya shiga taitayinsa – ‘Yan Majalisar hamayya

Marasa rinjaye a majalisar wakilai sun sa baki a game da tsige Elder Simon Achuba da ‘yan majalisar dokoki su ka yi daga kujerar mataimakin gwamnan jihar Kogi a cikin kwanakin nan.

‘Yan majalisar adawa sun yi Allah-wadai da maye gurbin Simon Achuba da Edward Onoja ba tare da bin doka ba. Shugaban marasa rinjaye a majalisa watau Ndudi Elumelu ya bayyana wannan.

A wani jawabi da Honarabul Ndudi Elumelu ya fitar a Ranar 23 ga Oktoba a madadin sauran ‘yan adawa a majalisar wakilan, ya nemi shugaban kasa dawo da gwamnan Kogi cikin hankalinsa.

Elumelu yake cewa: “An sabawa dokar kasa.” Ya kuma kara da gargadin mutanen Kogi cewa su shiryawa: “Salon mulkin zalunci da handama idan Bello ya kafa gwamnati maras farin jini.”

“Sauke mataimakin gwamna karshen cin mutuncin doka ne. Kasurgumin kama-karya ne. Dokar kasa da tsarin mulki ba su san wannan ba. Bai kamata a na ji, a na gani a kyale wannan ba.”

KU KARANTA: Rikicin APC ya sa an dakatar da Sakataren Jam'iyya a Edo

Jawabin ya ce: “Da wannan kutun-kutun na tsige mataimakin gwamna duk da cewa ‘bai da laifi’ kamar yadda kwamitin da ta bincikesa ta fada, ya nuna cewa mutanen nan ba su son doka ba.”

“Tasirin wannan shi ne an kakabawa mutanen jihar Kogi mataimakin gwamnan da doka ba ta san da shi ba, kuma wannan ba zai daure ba.” Elumelu ya kira gwamnatin Bello da wanda ta gaza.

Abin farin cikin shi ne wannan gwamnati za ta zo gaban kotun jama’a a Ranar 16 ga Watan Nuwamba inda mu ka yi amanna da mutanen Kogi cewa za su yi waje da wannan gwamnati.

Jawabin ‘yan majalisar ya kare da: “Mu na kiran shugaba Muhammadu Buhari da jam’iyyar APC ta sauka daga wannan giyan mulki domin tsarin farar hula ne kurum zai tabbatar da bin doka.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel