Jihohi 3 ne kadai su ke tsaye daram-dam-dam da kafafunsu a Najeriya

Jihohi 3 ne kadai su ke tsaye daram-dam-dam da kafafunsu a Najeriya

Wani bincike da aka yi ya nuna cewa mafi yawan Jihohi Najeriya ba za su kai labari idan har gwamnatin tarayya ta daina ba su kasonsu na FAAC wanda gwamnatocin kasar ke rabawa ba.

Jihohi 33 a za su yi iya biyan albashin ma’aikata daga abin da su ke samu da kansu ba. Wani bincike da hukumar BudgIT ta yi ya bayyana wannan. An wallafa rahoton wannan binciki a jiya.

A Ranar Laraba, 24 ga Watan Oktoba BudgIT ta wallafa rahoton da ya nuna cewa da za a janye kason FAAC, jihohi 3 ne rak za su iya daukar nauyin kansu ba tare da sun yi wasu ayyuka ba.

Wadannan jihohi su ne Legas, Akwa-Ibom da Ribas kamar yadda BudgIT ta bayyana. Babban Jami’in binciken wannan hukuma, Orji Uche, shi ne ya fitar da wannan rahoto mai ban tsoro.

Ko da za a samu bacin rana a ce wadannan jihohi ba su samu ko sisi daga asusun gwamnati na FAAC ba, jihohin nan za su ci da kansu albashin ma’aikata da sauran hada-hadan yau da gobe.

KU KARANTA: An samu sabani tsakanin Gwamnatin Buhari da Majalisa kan cin bashi

Mista Orji Uche ya kuma bayyana cewa duk da gudumuwar da jihohi da kananan hukumomi su ke samu daga hannun gwamnatin tarayya, jihohi 19 ne kadai ke iya rayuwa ba tare da bashi ba.

Jiha irin Delta mai arzikin man fetur ba za ta iya ci da kanta da abin da ta ke samu a karon kan ta. Jihohin Neja-Delta dai sun fi kowa kashe kudi wajen biyan albashi saboda karin arzikin mai.

Abin da Delta ta ke batarwa a wata ya haura biliyan 200. Jihar Bayelsa ta na kashe biliyan 137 kan albashi da sauransu a duk wata. Jihohin yankin na samun 13% na duk arzikin man fetur dinsu.

A Arewa kuwa nauyin da ke kan Sokoto, Jigawa da Yobe bai wuce biliyan 38, 43, 35 ba. Karyewar farashin danyan mai a kasuwar Duniya zai sa wadannan jihohi su gamu da kalubalen tattali.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel