Hattara jama’a: Sojojin Najeriya zasu yi gwaje gwajen makamai a jahar Kaduna

Hattara jama’a: Sojojin Najeriya zasu yi gwaje gwajen makamai a jahar Kaduna

Rundunar Sojan kasa ta Najeriya ta sanar da jama’a, musamman wadanda suke yankin Kachia da kewaye cewa za ta aika da dakarunta da kuma makamai zuwa wannan yanki a shirinta na gudanar da wani atisaye mai taken Exercise Vulcan Glow VII a ranar 28 ga watan Okoba.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito mataimakin daraktan hulda da jama’a na rundunar, Kyaftin Mohammed Maidawa ne ya sanar da haka a garin Kaduna a ranar Laraba, 23 ga watan Oktoba.

KU KARANTA: Kasar Rasha za ta shimfida ma Najeriya titin jirgin kasa mai tsawon kilomita 1,400

Don haka kyaftin Mohammed ya yi kira ga jama’a da kada su firgita idan sun ji karan harbe harbe, sa’annan ya gargadesu dasu kauce daga shiga yankin da za’a gudanar da wannan atisaye tun daga ranar 28 ga watan Oktoba zuwa 1 ga watan Nuwamba.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shi yana cigaba da fadin akwai taron janye wasu manyan hafsoshin Soji da suka hada da tsofaffin kwamandoji, manjo janar da Birgediya janar da zasu yi ritaya daga aiki, da zai gudana a cibiyar makamai ta Soji dake garin Kachia a ranar 2 ga watan Nuwamba na shekarar 2019.

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jaddada aniyarsa ta sabunta alakar Soji da kasar Rasha, wanda yace ta samo asali kimanin shekaru 59 da suka gabata tun bayan samun yancin Najeriya a shekarar 1960.

“Ta haka ne zamu samu daman sayen makaman Soja cikin sauki da kuma Sojojinmu su samu horo ingantacce tare da sabunta makaman Najeriya zuwa na zamani kamar yadda Putin ya yi alkawari.” Inji Buhari.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel