Kasar Rasha za ta shimfida ma Najeriya titin jirgin kasa mai tsawon kilomita 1,400

Kasar Rasha za ta shimfida ma Najeriya titin jirgin kasa mai tsawon kilomita 1,400

Gwamnatinkasar Rasha ta dauki alkawarin shimfida ma Najeriya layin dogo mai tsawon kilomita 1,400 tun daga jahar Legas har zuwa birnin Calabar dake yankin kudu maso kudancin Najeriya, inji rahoton Daily Nigerian.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kaakakin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Garba Shehu ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a babban birnin tarayya Abuja, inda yace wannan na daga cikin yarjejeniyar da Buhari ya kulla da shugaban Rasha Viladmir Putin.

KU KARANTA: Kwana 10 muka yi muna kirga kudin da tsohon gwamna Fayose ya kawo – manajan banki

Malam Garba ya cigaba da cewa shuwagabannin biyu sun sake tattaunawa a kan bukatar cigaba da aikin samar da tashar makamashin nukiliya a Najeriya, har ma shugaba Putin ya tabbatar ma Buhari cewa abin da ya rage kawai shine su fara aikin gina wannan tasha.

Haka zalika, dangane da alakar Soji tsakanin kasashen biyu, shugaba Buhari ya bayyana bukatar sake karfafa wannan tsohuwar alaka da aka faro tun shekaru 59 da suka gabata, wanda a baya ta yi sanyi.

“Na umarci ministan tsaro ya yi tare da ministan sharia domin tabbatar an karfafa wannan alaka ta soja tsakanin kasashen biyu cin dan kankanin lokaci sakamakon ta haka ne zamu samu daman sayen makaman Soja cikin sauki da kuma Sojojinmu su samu horo ingantacce tare da sabunta makaman Najeriya zuwa na zamani kamar yadda Putin ya yi alkawari.” Inji Buhari.

Daga karshe sanarwar ta bayyana cewa shuwagabannin biyu sun tattauna batutuwan da suka shafi ilimi da noma, inda Putin ya yi alkawarin kara adadin guraben tallafin karatu da kasar Rasha take baiwa yan Najeriya.

Haka zalika shima shugaba Buhari ya nemi tallafin kasar Rasha ta bangaren noman alkama, musamman duba da cewa kasar Rasha ce kan gaba wajen noman alkama a duniya, kuma nan take Putin ya amsa ma Buhari.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel