Buhari ya yi alkawarin narkon azaba ga bata-garin Malaman da ke ba Jami’a kunya

Buhari ya yi alkawarin narkon azaba ga bata-garin Malaman da ke ba Jami’a kunya

- Za a bi ta kan duk Malamin da aka kama ya na lalata da ‘Dalibai a Najeriya

- Shugaba Muhammadu Buhari yace za a rika hukunta masu wannan ta’adi

- Shugaban kasar ya yi alkawarin mummunar ukuba ga duk wanda aka kama

A jiya Ranar Laraba shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce Malaman jami’an da aka kama su na amfani da ‘Dalibai da nufin su ci jarrabawar makaranta, za su dandana kudarsu a kasar.

Shugaban kasar ya yi wannan jawabi ne a wajen yaye ‘Daliba jami’an jami’ar Ilorin watau UNILORIN a Ranar 23 ga Watan Oktoba. Cewar Jaridar The Nation.

Wani babban jami’in hukumar NUC mai kula da jami’o’i a Najeriya, Dr. Suleiman Ramon-Yusuf, shi ne ya wakilci shugaban kasar a wannan biki da jami’ar tarayyar da ke Garin Ilorin ta shirya.

KU KARANTA: Dubun wani katon-kawai da ke shiga gidan mata ta cika

Ramon-Yusuf, wanda shi ne mataimakin Darekta na hukumar, ya bayyana cewa wannan danyen aiki na rashin tarbiya da da’a da wasu tsirarrun Malamai su ke yi, ya na batawa jami’o’i suna.

“Babu shakka jami’o’in mu za su iya aiki ba tare da sun jawowa kansu mummunan maganar da ke yawo a Duniya yanzu na lalata da tursasa yaran makaranta domin samun sa’a a jarrabawa ba.”

“Abin takaici ne ace yayin da wasu Ma’aikatan jami’a ke kokarin ganin darajar makarantun Najeriya sun yi sama a nan gida da Duniya, bakin aikin wasu tsirarru ya na kokarin rufe wannan.”

Shugaban kasar yace wadannan bakaken ashana su na jawo abin kunya, ya kuma kara da cewa: “Daga yanzu duk wanda aka kama zai fuskanci mafi munin azabar da doka ta yi masa tanadi.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel