Kano 9: An ci zarafin daya daga cikin yaran 9 da aka sace

Kano 9: An ci zarafin daya daga cikin yaran 9 da aka sace

- Cibiyar binciken cin zarafi ta jihar Kano, ta gano cewa, an ci zarfain daya daga cikin yara 9 da aka sata a jihar aka kaisau Anambra

- Yarinyar mai shekaru 10 ta bayyana cewa, an yi mata fyade babu adadi a inda aka saceta

- Iyayen yarinyar, wadanda suka bukaci a boye sunansu, sun ce ba zasu kyale ba, zasu bi mata hakkinta

Kamar yadda cibiyar binciken cin zarafi ta jihar Kano ta gano, daya daga cikin yara 9 da aka sace a jihar kano aka samosu a jihar Anambra anyi mata fyade so da yawa a hannun wadanda suka saceta.

Shugaban cibiyar, Nasiru Garko, ya bayyana hakan ga jaridar Kano Focus bayan dubawar da aka yiwa yarinyar mai shekaru 10 kacal a duniya.

Ya ce, yarinyar ta bayyana cewa, anyi mata fyade a hannun wadanda suka saceta.

KU KARANTA: Duba hoton hadadden gidan da Mustapha Naburaska

Garko, wanda likita ne, ya ce binciken da yayi ya tabbatar da cewa abinda yarinyar ta fada gaskiya ne.

An kirkiro da cibiyar ne a asibitin Murtala da ke Kano don bincikar yara da ake cin zarafi.

Kawun yarinyar da bin ya auku a kanta, wanda ya bukaci da a boye sunansa,y ace zasu nemi taimakon sharfi’a don bin hakkin yarinyar.

Ya ce zasu yanke shawar akan bin hakkin yarinyar bayan an kamala shari’a tare da hukunta wadanda suka sace yaran.

Idana bazamu manta ba, a cikin watan da ya gabata ne aka samo yara 9 daga jihar Anambra wadanda aka sace a Kano kuma aka canza musu sunaye da addini.

Hakan kuwa ya jawo hankulan hukumomi, shuwagabanni da mutane masu fada aji.

A hakanne kuwa gwamnatin jihar Kano da ta tarayya suka yi alkawarin yi wa yaran adalci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel