Malami ya bukaci 2.5% na kudin Abacha don amfanin ofishinsa

Malami ya bukaci 2.5% na kudin Abacha don amfanin ofishinsa

- Ministan shari'a na Najeriya, Abubakar malami, ya bukaci majalisar tarayyya da ta aminta ofishinsa ya karba kashi 2.5% na kudaden Abacha

- Kamar yadda ya bayyana gaban majlisar dattawa, ya ce hakan zai assasa karbo ragowar kudaden

- 'Yan majalisar sunaminta da hakanamma sun bukaci da ya tura bukatar ga majalisar a rubuce

Ministan shari’a na Najeriya, Abubakar Malami ya bukaci majalisar tarayya da ta aminta cewa ofishinsa ya karba kashi 2.5 na kudin Abacha.

Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da gurfana a gaban kwamitin majalisar na shari’a, kare hakkin dan adam da lamurran shari’a don kare kasafin kudi shekarar 2020 na ma’aikatarsa.

“A hankali muke ta samu kudadenmu da aka handame aka adana a kasar waje. Inaso in tabbatar muku da cewa, duk wasu hanyoyi da shari’a ta tanadar don karbo kudaden suna da wuya kuma da yawa,” in ji shi.

KU KARANTA: Dalilin da ya hana jaruma Maryam Yahaya aure

“A lokuta da dama sai mun samu kwararrun lauyoyi tare da masu bada shawarwari na musamman don samo kudaden. Don saukake lamarin, akwaqi bukatar kafa kwamitin samo kudaden da aka handame a ofishina,”

“Inaso in kara jaddada bukatata da a mika 2.5% na kudaden da aka samo don amfanin ofishina. Zamuyi amfani da kudaden don ganin mun biya kwararrun lauyoyi da masu bada shawara na musamman da ma’aikatar ke amfani dasu.”

An zargi Malami da jagorar biyan lauyoyi dala miliyan 15 daga cikin kudaden da aka samo wadanda Abacha ya handame. Biyan kudaden kuwa ya jawo cece-kuce saboda dai lauyoyin Basu cancanci kudaden da aka loda musu ba tunda da yawan aiyukan lauyoyin Swiss ne suka yi shi.

'Yan majalisar sun goyi bayan hakan amma sun bukacoi da ya tura ga majalisar a rubuce gudun zargi don bay a ciukin kasafin kudin shekarar 2020.

A jawabinsa, Chukwuka Utazi, ya goyi bayan bukatar tare da cewa, hakan zai sa ayi saurin samun kudaden kuma akan lokaci.

Dan majalisar ya jinjinawa Malami akan jajircewarsa tare da kokarinsa akan aikin kasarsa tun a shekarar 2015.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel