Gidauniyar Sanatan APC ta ware biliyan domin tallafa wa yaran da basa zuwa makaranta

Gidauniyar Sanatan APC ta ware biliyan domin tallafa wa yaran da basa zuwa makaranta

Gidauniyar tsohon gwamnan Imo kuma sanata a APC, Rochas Okorocha, ta ware naira biliyan daya (N1bn) domin shawo kan kalubalen yawan yaran da basa zuwa makaranta a fadin Najeriya.

Ucy Rochas, darektan janar ta gidaubiyar Rochas, ita ce ta sanar da hakan ranar Laraba yayin da take gana wa da manema labarai.

Ta ce za a kaddamar da tsarin tallafa wa yaran a karkashin sabon aikin gidauniyar mai suna "Rochas Foundation Education And Development (READ) programme" wanda za a kaddamar a cikin shekarar 2020.

"Kamar yadda kuka sani, akwai kimanin yara miliyan 10 da basa iya zuwa makaranta saboda talauci, yawancin irin wadannan yara suna yawo, suna gararambar neman abinda zasu ci a kan tituna da lunguna na fadin kasar nan.

"Gidauniyar Rochas ta yi kasafin kudi har Naira biliyan daya domin tallafa wa irin wadannan yara, za a raba wa kungiyoyin aikin jin kai da aka yarda da su kudin domin ganin sun shiga lunguna da sako na kasar nan.

DUBA WANNAN: Adam Zango ya kashe N46.75m wajen daukan nauyin karatun dalibai 101

"Hatta gwamnatin tarayya ta nuna damuwarta a kan wannan mummunar matsala kuma ta fara kokarin shawo kan lamarin.

"Gidauniyar Rocahas zata hada kai da ma'aikatar ilimi ta gwamnatin tarayya a tsakanin shekarar 2020 zuwa 2021 domin cimma manufar rage yawan yaran da basa zuwa makaranta a Najeriya," a cewar ta.

Ucy ta roki sauran kungiyoyi da hukumomi da su taimaka wajen yaki da yawan yaran da ake da su da basa zuwa makaranta, tare da bayyana cewa adadin yaran da basa zuwa makaranta ya yi yawan da ya kamata kowanne dan kasa cikin damu wa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel