Yariman Saudiyya Bin Salman zai sayi kulob din Ingila na Manchester United

Yariman Saudiyya Bin Salman zai sayi kulob din Ingila na Manchester United

- Yariman kasar Saudiyya Muhammed Bin Salman ya gama shiri tsaf domin sayen kulob din kasar Ingila na Manchester United

- An bayyana cewa Bin Salman ya taya kulob din Manchester United akan kudi Fam Miliyan Dubu Uku

- Dama dai Yariman ya taba yunkurin sayan Kulob din a shekarun baya aka ki sayar masa

Wasu rahotanni da muka samu sun bayyana cewa Yariman kasar Saudiyya Muhammed Bin Salman ya nemi a sayar masa da shahararren kulob din nan na kasar Ingila Manchester United akan kudi Fam Miliyan dubu uku.

Yanzu haka dai ana ta faman magana akan cewa da zarar Bin Salman ya samu nasarar sayan wannan kulob din yana da arzikin da zai iya sayen manyan 'yan wasa wanda suke da kwarewa a fannin kwallon kafa.

Kafafen yada labarai na kasar Ingila sun bayyana cewa dama can Yariman ya nuna yunkurin sayen kulob din amma Glazer Family masu kulob din suka nuna rashin amincewar su.

KU KARANTA: Kano ko da me ka zo an fika: An bude gidan sayar da abincin Naira 30 a jihar Kano

Glazer Family dai sune suke da kaso mafi tsoka a cikin kulob din inda kuma suka yi yadda su sayarwa da Yariman kason su.

Bincike ya bayyana cewa Bin Salman yana matukar kishin masarautar hadaddiyar daular larabawa ganin cewa ita take mallakar kulob din Manchester City.

An bayyana cewa idan har Bin Salman ya yi nasarar sayan kulob din to zai sayi 'yan wasa kamar su Koulibaly, Chilwell, Toni Kross, James Maddison, Jadon Sacho da Timo Werner.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel