Kwana 10 muka yi muna kirga kudin da tsohon gwamna Fayose ya kawo – manajan banki

Kwana 10 muka yi muna kirga kudin da tsohon gwamna Fayose ya kawo – manajan banki

Tsohon manajan reshen bankin Zenith dake garin Akuren jahar Ondo, Sunday Alade ya bayyana ma babbar kotun tarayya dake zamanta a jahar Legas cewa kwanaki 10 cur suka kwashe suna kirga naira biliyan 1.2 da Fayose ya kai musu ajiya.

Jaridar Punch ta ruwaito Sunday ya gurfana a gaban kotu ne a matsayin shaidan hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC a shari’ar da take yi da Fayose a kan zargin satar naira biliyan 2.2.

KU KARANTA: Matasan Arewa zasu yi zaman dirshan a kan tituna idan Buhari bai tabbatar da Magu ba

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a zaman kotun na ranar Laraba, 23 ga watan Oktoba, Sunday ya bayyana mata cewa a watan Yuni na shekarar 2014 ne Fayose ya aiko wani hadiminsa Abiodun Agebele da kudaden domin ya zuba masa a asusunsa na bankin.

Sunday ya kara da bayyana ma kotu cewa jiragen sama guda biyu ne suka dauko kudaden, sa’annan aka yi amfani da wata babbar motar bankin ta daukan kudi wajen kwashe kudaden daga jiragen a cikin sawu biyu zuwa bankin.

“A sawun farko, mun dauki naira miliyan 744, a sawu na biyu kuma naira miliyan 494, jimilla naira biliyan 1.2 kenan, kudin sun samu rakiyar mutane uku ne, daga cikinsu har da wani mai suna Adewale O wanda ya bayyana kansa a matsayin hadimin Sanata Musliu Obanikoro.

“Sai da muka kirga kudin don tabbatar da adadinsu, kwanaki goma ya dauki jami’anmu suna wannan aikin, bayan nan muka sanya kudaden cikin asusun bankuna guda uku.” Inji shi.

Shima wani babban jami’in babban bankin Najeriya, Aliu Muhammed ya bayyana cewa CBN ta aika naira biliyan 2.2 daga asusun bankin tsohon mashawarcin shugaban kasa a kan harkar tsaro, Sambo Dasuki zuwa asusun bankin Diamon mallakin wani kamfanin Sylva Mamanara.

Bayan sauraron wadannan dogayen jawaban, mai shari’a Aneke ya dage shari’ar uwa ranar Juma’a, 25 ga watan Oktoba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel