Ministan Buhari ya mayar da wasu makuden kudi da aka tura wa ma'aikatansa kan kuskure

Ministan Buhari ya mayar da wasu makuden kudi da aka tura wa ma'aikatansa kan kuskure

Ministan Wasanni, Sunday Dare ya bayar da umurnin mayar da $130,000 (47,058,298.18) da Kungiyar Masu Wasannin Motsa Jiki na Kasa da Kasa (IAAF) ta biya cikin wani asusun ajiyar sashi na ma'aikatan a 2017.

Bayan ta dade tana yunkurin karbo kudin, Kungiyar ta IAAF ta yi barazanar saka wa Kungiyar Masu Wasannin Motsa Jiki ta Najeriya (AFN) takunkumi.

A cikin wasikar da ya aike wa shugaban AFN, Ibrahim Gusau, Jee Isram, babban Manaja na IAAF, ya ce hukumar ta tuntubi AFN nan take bayan an gano kuskuren a Maris din 2018 amma Najeriya ba ta mayar da kudin ba.

DUBA WANNAN: Da duminsa: FG ta canja wa ma'aikatar sadarwa suna

Amma a yammacin ranar Laraba a shafin Twitter, Dare ya ce duk da la'akari da jinkiri da ake samu wurin aike da kudi tsakanin bankunna mabanbanta, kudin zai shiga asusun IAAF cikin kwanaki kadan.

Ya rubuta, "IAAF - Na bayar da umurnin mayar da kudaden da IAAF ta tura asusun Kungiyar Masu Wasannin Motsa Jiki ta Najeriya. Nan da 'yan kwanaki kudin zai shiga asusun IAAF duba da cewa a kan samu jinkiri wurin tura kudi tsakanin mabanbantan bankuna. Hakan zai dawo wa Najeriya mutuncin ta."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel