'Yan sanda sun gurfanar da mutumin da ya kashe Mata 10

'Yan sanda sun gurfanar da mutumin da ya kashe Mata 10

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta gurfanar da wani mutum mai suna Gracious David-West bayan ya amsa cewar ya kashe Mata 10 kamar yadda ake zarginsa da aikata wa.

Da yake magana a gaban alkalin kotun da aka gurfanar da shi bayan an gurfanar da shi, David-West ya ce, "mai girma mai Shari'a, na kashe mata guda 9 a Otal, sai wata guda daya, cikon ta 10, wacce ban samu ikon kashe ta ba, amma na daure ta a jikin kujera."

Sai dai, ya nemi afuwa bayan ya amsa laifuka 9 daga cikin 10 da ake tuhumarsa da aikata wa tare da bayyana cewa ya aikata laifukan ne bisa rudin shaidan.

DUBA WANNAN: Da duminsa: FG ta canja wa ma'aikatar sadarwa suna

David-West ya bukaci kotun ta umarci rundunar 'yan sanda ta mayar masa da kudinsa N60,000, sarka da agogonsa da suka kwace a hannunsa.

Yanzu haka gwamnatin jihar Ribas, a karkashin ofishin kwamishinan Shari'ar, Zacchaeus Adango, ta karbi ragamar cigaba da Shari'a tuhumar David-West.

Alkalin kotun, Jastis Enebeli, ya amince da bukatar gwamnatin jihar tare da lasar takobin ganin ba a samu tsaiko a Shari'ar ba kafin daga bisani ya daga sauraron Shari'ar zuwa ranakun 18, 21, 27 da 29 ga Nuwamba, yayin da za a cigaba da tsare David-West a gidan yari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel