Majalisar dokokin Nasarawa ta tabbatar da zababbun kwamishinonin Gwamna Sule

Majalisar dokokin Nasarawa ta tabbatar da zababbun kwamishinonin Gwamna Sule

Majalisar dokokin jihar Nasarawa ta tantance tare kuma da tabbatar da zababbun kwamishinoni 15 da gwamna Abdullahi Sule ya aika masu.

Kakakin majalisar, Mista Ibrahim Abdullahi ne ya bayyana haka a ranar Talata bayan kammala tantancewar kwamishinoni shida, wadanda suka bayyana don tantancewa a zauren majalisar dokokin a Lafia.

Abdullahi yace “idan muka tuna a baya, a ranar Litinin, majalisar ta tantance Ahmed Yahaya (karamar hukumar Toto), Philip Dada (karamar hukumar Karu), Othman Adam (karamar hukumar Keffi), Dr Abdulkarim Kana (karamar hukumar Kokona), Obadiah Boyi (karamar hukumar Akwanga), Yusuf Turaki (karamar hukumar Awe), Dr Salihu Alizaga (karamar hukumar Nassarawa Eggon), Dogo (karamar hukumar Wamba) da kuma Farfesa Otaki Allahnanah (karamar hukumar Keana).

“A yau mun tantance sauran kwamishinoni shida da aka gabatar. Sun kasance Haruna Adamu (karamar hukumar Obi), Ibrahim Ekye (karamar hukumar Doma), Misis Fati Sabo (karamar hukumar Nasarawa), Abubakar Imam(karamar hukumar Lafia), Hajiya Halima Jabiru (karamar hukumar Lafia) da kuma Mohammed Aliyu (karamar hukumar Lafia).

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun yi garkuwa da jami’in sufuri na gidan gwamnatin Taraba

“Wadannan kwamishinonin da muka tantance a ranar Litinin, 21 ga watan Oktoba da Talata, 22 ga watan Oktoba, majalisar ta tabbatar da su bayan ta ga cancantarsu a mukaman.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel