Karin albashi: A biya Ma’aikata kudinsu kafin karshen Disamba - FEC

Karin albashi: A biya Ma’aikata kudinsu kafin karshen Disamba - FEC

- Majalisar zartarwa ta FEC ta nemi Ministar kudi ta fara shirin biyan sabon albashi

- FEC ta umarci Zainab Ahmed ta soma biyan wannan kudi ne kafin 31 ga Disamba

- Ngige yace sabon albashin zai fara aiki ne tun daga Ranar 18 ga Watan Afrilun nan

Mun samu labari cewa majalisar FEC ta zartawa a Najeriya ta umarci Ministar kudi, Zainab Ahmed, ta tabbatar da cewa an soma biyan ma’aikata sabon karin da aka yi kafin Disamba 31.

Ministan kwadagon Najeriya, Dr. Chris Ngige, shi ne wanda ya bayyana wannan a lokacin da ya zanta da Manema labarai a fadar shugaban kasa da ke Abuja a Ranar Laraba, 23 ga Oktoba, 2019.

Chris Ngige ya yi wannan jawabi ne jim kadan bayan mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ya jagoranci taron FEC na Ministoci wanda aka saba zama duk Ranar Laraba a fadar Aso Villa.

KU KARANTA: Osinbajo ya jagorancin zaman FEC yayin da Buhari ya tafi Rasha

Dr. Ngige ya bayyana cewa majalisar tarayyar ta cin ma matsayar cewa a fara biyan ma’aikata sabon albashi na akalla N30, 000 daga yanzu har zuwa Ranar Talata 31 ga Watan Disamban 2019.

Bayan haka Ministan ya sanar da cewa sabon tsarin albashin zai fara aiki ne daga Ranar 18 ga Watan Afrilu. Hakan na nufin ma’aikata za su bi gwamnati bashin duk wadannan tarin watanni.

Ministan harkokin jirgin sama, Hadi Sirika ya bayyana cewa an yi na’am da Naira biliyan 1.7 da aka ware domin wasu ayyuka da za a yi a filin hawa da tashin jirgin sama da ke Zaria da Katsina.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel