Kwallon kafa: Real Madrid ta fara tuntubar tsohon Kocinta Jose Mourinho

Kwallon kafa: Real Madrid ta fara tuntubar tsohon Kocinta Jose Mourinho

Rade-rade su na yawo cewa kungiyar Real Madrid ta tuntubi Jose Mourinho yayin da ta fara tunanin kawo wanda zai maye gurbin Mai horas da ‘yan wasanta a halin yanzu.

Kamar yadda mu ka ji labari, Real Madrid ta tado da wannan magana ne bayan kungiyar ta sha kashi a gaban ‘yan kallonta a hannun kungiyar Real Mallorca a Gasar La-liga.

Nasarar da Mallorca ta samu a kan Real Madrid shi ne wasan farko da Kungiyar ta rasa a gasar cin kofin gida. Sai dai duk da haka kulob din na ta faman gaba da baya a kakar nan.

A cikin farkon makon nan ne jaridar El Chiringuito ta rahoto cewa Real Madrid ta tuntubi Jose Mourinho da nufin duba yiwuwar ko zai iya dawowa kungiyar da ya bari a baya.

KU KARANTA: Zargin fyaden Ronaldo shekaru goma da su ka wuce ya farfado

Fitaccen kocin Duniya Jose Mourinho ya horas da Real Madrid daga 2010 zuwa cikin kakar 2013. Tsohon kocin na Inter ya rabu da kungiyar ne bayan sun samu wasu sabani.

Kishin-kishin komawar Mourinho Madrid ya na kara karfi watanni bakwai rak da Zinedine Zidane ya karbi ragamar Real Madrid bayan ya ajiye aikinsa a tsakiyar shekarar 2018.

Duk da karfin wannan jita-jita, Mourinho mai shekara 56 a Duniya bai fito ya yi magana game da sha’awarsa na sake horas da kungiyar Real Madrid a daidai wannan marra ba.

Shi kuma Kocin ya bayyana cewa babu abin da ke tada masa hankali a kungiyar da ya dade tun yana ‘dan wasa. Zinedine Zidane ya yi watsi da surutun cewa yana cikin matsala.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel