Ka gyara kura-kuran kasafin kudinka, ka dawo – Majalisa ta fadawa AGF

Ka gyara kura-kuran kasafin kudinka, ka dawo – Majalisa ta fadawa AGF

Majalisar wakilan tarayya ta nemi shugaban Akawun Najeriya watau Akanta Janar na gwamnatin tarayya, Ahmed Idris, ya shawo kan matsalolin da aka samu a cikin kasafin kudin shekarar 2020.

Shugaban kwamitin kudi a majalisar wakilan tarayya Honarabul James Faleke da sauran ‘yan kwamitin sun duba kasafin kudin da Akanta Janar na kasar ya gabatar a cikin farkon makon nan.

Kamar yadda mu ka samu labari daga jaridar Daily Trust, ‘yan kwamitin sun gano kura-kurai a cikin kasafin AGF inda James Faleke ya nemi babban Akawun ya gabatar masu da wasu takardu.

Kwamitin sun bukaci Idris Ahmed ya bada bayanin kudin da ma’aikatu su ka kashe daga Watan Junairu zuwa Oktoban bana. Za a yi bincike na musamman ne kan masu tatsowa gwamnati kudi.

KU KARANTA: Gwamnatin Tarayya ta canzawa Ma'aikatar sadarwa suna

Bayan haka ‘yan majalisar sun bukaci Akawun gwamnatin ya bada rahoton kashi 25% da ma’aikatu da hukumomi su ke maidawa cikin asusun gwamnatin tarayya daga 2014 zuwa yau.

‘Yan majalisar sun dauki wannan mataki ne domin gano hukumomin da ke karbar kudi da sunan gwamnatin tarayya amma su yi mursisi. Hakan na zuwa ne bayan an gabatar da kasafin 2020.

Honarabul Faleke ya fadawa Ahmed Idris ya yi maza ya yi gyare-gyaren da su ka kamata a cikin kasafin kudin na sa, ya dawo da shi gaban majalisa domin a sake dubawa, a kuma amince da shi.

A halin yanzu dai kwamitocin majalisa su na aiki ne a kan kundin kasafin kudin badi. A Ranar 21 ga Watan Oktoban ne aka fadawa Ministan Neja-Delta ya koma ya gyara kasafin ma’aikatarsa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel