ICPC ta cafke jami'an FRSC 26 kan karbar kudi ta 'karfi da yaji' daga mutane

ICPC ta cafke jami'an FRSC 26 kan karbar kudi ta 'karfi da yaji' daga mutane

Jami'an Hukumar Yaki da Rashawa ta ICPC, sun kama jami'an Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa, FRSC guda 26 yayin wata simame da suka kai tare da hadin gwiwan wasu hukumomin gwamnatin tarayya.

Sanarwar da mai magana da yawun ICPC, Rasheedat Okoduwa ta fitar ya ce an kama jami'an ne saboda samunsu da laifin yunkurin karbar kudi daga hannun masu ababen hawa a tittunan Najeriya bayan Hukumar ta FRSC ta yi korafi.

Sanarwar ta ce, "Sauran hukumomin gwamnati da aka shirya simamen da su da aka saka wa suna Operation Tranquility sun da hada da FRSC da DSS. Yayin simanen a Owerri a jihar Imo, an kama wani mutum da ake zargi shine ma'ajin wadanda ke kwatan kudin matafiyan."

DUBA WANNAN: Kwastam sun gano wani gida da ake canjawa shinkafa buhu, sun kama mutum 15 (Hoto)

The Punch ta ruwaito cewa an gudanar da sumanen ne a jihohin Imo, Zamfara, Ondo da Yobe.

Kididigan wadanda aka kama ya cewa an kama jami'an FRSC tara da farar hula daya Owerri, jihar Imo; Jami'an FRSC takwas a Kaura-Namoda, jihar Zamfara; wasu jami'an biyar a Ore a jihar Ondo; da kuma hudu a Potiskum na jihar Yobe.

Sanarwar ta kara da cewa, "An gano kudade masu yawa a tare da jami'an na FRSC da aka kama da kuma wani farar hulan kafin a mika su hannun ICPC."

"An bayar da belin dukkan jami'an na FRSC da farar hular da aka kama kafin zuwa lokacin da hukumar za ta kammala bincike a kai su kotu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel