Dalilin da ya sa mu ka nemi hadawa da addu’a wajen yaki da Boko Haram – Buratai

Dalilin da ya sa mu ka nemi hadawa da addu’a wajen yaki da Boko Haram – Buratai

Shugaban rundunar sojojin Najeriya, Laftanal Janar Tukur Buratai, ya bayyana cewa rundunar sun nemi hadawa da addu’o’i wajen yakar yan ta’addan Boko Haram ne saboda a yi nasarar dakile yadda kungiyar ke farfaganda.

A cewar Buratai wanda ya samu wakilcin Birgediya Janar Timothy Olowomeye a wajen wani taron horar da limaman kiristoci a jihar Sokoto, sun nemi hadawa da wa’azai da addu’o’i wajen yakar Boko Haram da sauran masu tayar da hankula.

“Yin amfani da makami kadai da sojoji ba zai iya kakkabe Boko Haram ba. Idan aka samu wata kwakkwarar hanyar da a yaye musu mummunar akidar da ake cusa musu, zai yi tasiri sosai a kan su da mummunar akidar rikau mai zafi da aka cusa musu a kwakwalwar su,” inji shi.

Buratai ya ce Najeriya da sauran kasashen duniya da dama sun dade su na fama da tashe-tashen hankula da ke da nasaba da addini, tattalin arziki da wadanda ke da dalilai na siyasa.

KU KARANTA KUMA: San barka: Jarumi Adam A Zango ya ware kimanin miliyan 47 domin daukar nauyin karatun dalibai 101

Ya kara da cewa imanin da ‘yan Boko Haram suka yi shi ne har yau ya zama dole a rika hadawa da bangaren addini aka warware mummunan tunanin da ake cusa wa matasa a kwakwalwar su.

Ya yi fatan taron zai inganta dukkan hanyoyin da za a bi wajen wanke kwakwalwar wadanda ake cusa wa mummunar akidu na addini.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel