Zaben Bayelsa: Kar muke kallonku, hukumar tsaron DSS ta gargadi ‘yan siyasan Bayelsa

Zaben Bayelsa: Kar muke kallonku, hukumar tsaron DSS ta gargadi ‘yan siyasan Bayelsa

Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta gargadi ‘yan siyasar jihar Bayelsa inda ta ce tana lure da su bisa zaben gwamnan jihar Bayelsa dake tafe ranar 16 ga watan Nuwamba.

DSS ta ce ta sanay ido ne a kan ‘yan siyasan domin ganin ko akwai wani daga cikinsu wanda zai yi kokarin tayar da zaune tsaye a lokacin zaben gwamnan.

KU KARANTA:Fintiri ya zabi dandan Atiku da wasu mutum 22 a matsayin kwamishinoninsa

Da ya ke magana a wurin wani taron fadakarwa da hukumar ‘yan sandan Najeriya ta shirya, Daraktan DSS na jihar Bayelsa, Ishaku Yusuf ya ce mutanen da aka sanyawa idon ‘yan siyasa ne wadanda kan iya tayar da rikici a lokacin zaben.

Mataimakin Sufeto janar na ‘yan sandan Najeriya mai kula da Zone 5, AIG D.P Yakadi ne ya jagoranci taron a jihar Bayelsa.

Yusuf ya ce: “Game da damke masu kokarin tayar da fitina a lokacin zaben gwamnan jihar mun zuba ido sosai ga ‘yan siyasar. Duk wani wanda muke zargin zai iya tayar da rikici idanunmu na kansa a duk inda ya ke.”

Haka kuma ya nuna rashin jin dadinsa saboda rashin halartar taron da aka shirya saboda su, inda yake cewa wannan alama ce dake nuna ba su shirya ma zaben gwamnan ba.

A cewarsa, cikin jam’iyyu 45 wadanda ke takarar gwamnan amma guda 10 kacal ne suka turo da wakilansu zuwa wurin taron.

A nashi jawabin kuwa, Yakadi ya fadi abubuwan da za su iya kawo rikici a lokacin zaben, kuma ya yi kira ga jam’iyyun siyasa da su guji aikata wadannan abubuwan domin ayi zaben lami lafiya.

https://thenationonlineng.net/dss-to-bayelsa-politicians-we-are-watching-you/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel