Da duminsa: Kotu ta dakatad da daukan sabbin yan sanda 10,000

Da duminsa: Kotu ta dakatad da daukan sabbin yan sanda 10,000

Alkali Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya dake Abuja a ranar Laraba ya dakatad da daukan sabbin yan sanda 10,000 da hukumar yan sanda ke kan yi.

Hukumar jin dadin yansanda wato Police Service Commission PSC ta shigar da kara da sifeto janar da hukumar yan sanda da ministan harkokin yan sanda kotu kan shirin daukan sabbin yan sanda ba tare da saninta ba.

PSC ta bukaci kotun ta haramtawa hukumar daukan sabbin mutane aiki saboda hakan ya sabawa kundin tsarin mulkin da ya kafa hukumar.

A makon da ya gabata, hukumar yan sanda ta bayyana cewa za'a saki sunayen wadanda suka samu nasara a atisayen daukan sabbin yan sanda.

Amma a yau (Laraba), kotu ta fadawa bangarorin biyu cewa a dakatad da komai.

An samu sa'insa tsakanin lauyoyi a kotun yayinda lauyan sifeton yan sanda, Alex Izinyon, ya laburtawa kotu cewa tuni hukumar ta kammala daukan sabbin yan sanda.

Daga karshe, Alkali Ekwo ya dage zama zuwa ranar 4 ga Nuwamba domin cigaba da sauraron karar da yanke shawara kan abinda zai faru.

SHIN KA KARANTA WANNAN Yanzu-yanzu: FG ta bada umurnin biyan ma'aikata karin mafi karancin albashi daga watan Afrilu zuwa yau

A farkon wannan watan, hukumar kula da yan sanda PSC ta yi fito na fito da sifeto janar IG Adamu kan shin wanene ke da hakkin daukan sabbin jami'an yan sanda 10,000 da shugaba Buhari yayi umurni.

Rahotanni sun bayyana cewa an dakatad da daukan sabbin yan sanda sai sun sasanta.

Mai magana da yawun hukumar, Ikechukwu Ani, a jawabin da ya saki ya tabbatar da cewa an dakatad da daukan yan sandan.

Ya umurci matasa masu neman aikin su saurari sakamakon da zai biyo baya kuma su yi watsi da wani jerin sunaye da aka fitar saboda ba sahihi bane.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel