Yan bindiga sun yi garkuwa da jami’in sufuri na gidan gwamnatin Taraba

Yan bindiga sun yi garkuwa da jami’in sufuri na gidan gwamnatin Taraba

Yan bindiga a safiyar ranar Laraba sun kai mamaya gidan Magami na jami’in sufurin gidan gwamnatin Taraba, Jalingo, Mista Danlami Yunana sannan suka dauke shi.

Wata kanwar jami’in sufurin da aka sace, Blessing Samuel ta fada ma manema labarai a Jalingo, cewa masu garkuwan sun kai mamaya gidan da misalin karfe 1:00am da 2:00am sannan suna ta harbi kafin suka tafi dashi.

“Sun zo su da yawa sannan suka harbi ainahin kofar shiga gidan domin samun damar shigowa.

“A hankali suka hauro ta Katanga domin shiga harabar gidan.

“A lokacin da na ji an kwankwasa kofa, sai na baro dakina domin nahe na bude, amma sai yayana Yunana ya hana ni, a lokacin ne suka fara harbiin ainahin kofar shigowa sannan suka shigo suka tisa keyarsa,” inji ta.

KU KARANTA KUMA: An tsare mutane 6 akan kisan wata yarinya yar shekara 3 a Kano

A halin da ake ciki, wata majiya ta ahlin gidan ta fada ma majiyarmu ta Punch cewa wadanda suka yi garkuwa da Danlami Yunana na neman a basu naira miliyan 50 a matsayin kudin fansa kafin su sake shi.

Da aka tuntube shi, kakakin yan sandan jihar Taraba, ASP David Misal yace ya samu labarin lamarin amma ba a riga an sanar dashi cikakken bayani ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel