An tsare mutane 6 akan kisan wata yarinya yar shekara 3 a Kano

An tsare mutane 6 akan kisan wata yarinya yar shekara 3 a Kano

Wata kotun majistare da ke zama a No-Man’s-Land a Kano ta tsare wasu mutane shida a gidan kurkuku kan zargin kasha wata yarinya yar shekara uku.

Wadanda ake zargin sune Abubakar Idris, 23, Usman Abdullahi, 22, Auwalu Yahuza, 28, Bashiru Ahmad, 28, Nura Inusa, 22 da kuma Abba Abubakar, 19, dukkaninsu mazauna Gaburawa Yanyashi Tudun Fulani, jihar Kano.

An gurfanar da su akan tuhume-tuhume uku na hada kai wajen ta’addanci, fashi da makami da kuma kisa wanda ya kara da sashi na 6 (d) (b) (c), 1 (1) (2) na dokar fashi Act cap RII LFN na 2004 da kuma sashi na 221 na doka.

Dan sanda mai kara, ASP Sani Musa ya fada ma kotu cewa wadanda ake zargin a ranar 2 ga watan Satumba da misalin karfe 11:00 na dare, sun kai mamaya gidan Abba Abdulmu’min na Yanyashi Tudun Fulani quarters.

Ya kara da cewa, “Bayan sun kai harin sannan suka yiwa matarsa, Malama Farida Shuaib fashin N170,000, wadanda ake zargin sun kuma yanka yar mai suna Shukura Abba Shuaibu yar shekara sannan suka jefar da ita cikin rijiya wanda hakan yayi sanadiyar mutuwarta.”

KU KARANTA KUMA: San barka: Jarumi Adam A Zango ya ware kimanin miliyan 47 domin daukar nauyin karatun dalibai 101

Yayinda aka karanto abubuwan da ake tuhumarsu akai, biyar daga cikinsu sun amsa tuhume-tuhume uku, yayinda mutum dayan da yayi saura yaki amsa dukkanin tuhumar da ake masa.

Alkalin kotun, Ibrahim Khalil Mohammed ya yi umurnin tsare wadanda ake zargin a gidan yari sannan ya dage shari’am zuwa 12 ga watan Nuwamba domin cigaba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel