Babbar magana: Yadda Malami na ya dinga kama mini nono yana neman lalata dani a cikin ofis din sa - Daliba ta tona asirin bunsurun malami

Babbar magana: Yadda Malami na ya dinga kama mini nono yana neman lalata dani a cikin ofis din sa - Daliba ta tona asirin bunsurun malami

- Wata budurwa ta bayyana halin da ta shiga bayan wani Malamin ta ya bukaci ya dauke ta aiki

- Ta bayyana cewa mintuna kadan da daukarta aikin ya nemi yayi lalata da ita

- Ta ce tun da ta samu ta fita daga ofishin sa ta tafi gida ba ta kara komawa ba

Kamar yadda jaridar Information Nigeria ta ruwaito wata dalibar jami'ar jihar Benin wacce ta nemi a boye sunanta, ta bayyana yadda ta sha fama da wani Malamin ta wanda ya nemi ya ba ta aikin yi a ofis din sa, mintuna kadan da bata aikin kuma ya nemi yayi lalata da ita.

Ga abinda dalibar ta ce:

"Mun je mu ofishin sa ni da kawata domin mu duba sakamakon jarrabawar mu. Sai ya tambaye mu lambar matirikulashin din mu muka gaya masa ya nuna mana sakamakon mu, duka ni da kawata mun samu sakamako mai kyau domin duk mun samu 'B'.

"Malamin ya ce yaji dadi sosai da irin kokarin da muke da shi ni da kawata, sai ya ja mu da hira.

"Sai dai kuma a cikin hiran naga kamar hankalin shi yafi dawowa kai na, domin duk kusan ni yake kallo, har yake tambayata idan ina so zai dauke ni aiki a ofishin sa na dinga taimaka masa da wasu abubuwan kafin lokacin tafiyar mu bautar kasa yayi.

"Ai kuwa cikin gaggawa na amince, sai dai kuma naga kamar kawata bata ji dadi ba, cikin kankanin lokaci na fara tunanin yadda wannan dama dana samu za ta taimaki rayuwata har na kai ga samun koyarwa a jami'a.

"Zaki fara zuwa aiki ba tare da bata lokaci ba, in ji shi.

"Sai muka fita waje nida kawata ta taya ni murna da sabon aikin dana samu ta wuce.

"Sai na dawo ofishin lakcaran na mu, ya fito da wasu takardu ya bani yace na fara taya shi aiki da su.

"Ai kuwa na fara aiki ba kama hannun yaro, banyi aune ba sai jin hannaye nayi akan nonuwa na.

"Da farko na kasa cigaba da abinda nake yi, na kasa motsawa kuma, sai naji dakyar nake numfashi, na ma rasa mai zance.

"Ban ji dadin wannan abu ba ko kadan, wannan mutumi shine nake kallo a matsayin abin koyi na tsawon shekara hudu, mutumin da a shekaru zai yi sa'an mahaifina, hasalima na zabi ajin shi ne saboda ina matukar ganin girman shi.

"Sai na daga kaina na kalle shi, sai yayi wata dariya ta mugunta ya dauke hannunshi daga jikina, a wannan lokacin naji duk wata kunya da girman shi da nake gani ta fita a raina. Na gode Allah na riga na gama karatu na babu abinda zai kara kawo ni wajen shi.

"Sai na nuna mishi babu damuwa na cigaba da aikina, sai yake ta faman yi mini tambayoyi ina ba shi amsa, ina ta addu'a lokacin ta shi daga aikin yayi.

"Da lokacin tashi yayi sai yace na wuce gida, ya bani dari biyar nayi kudin mota, naki karbar kudin duk da yayi ta rokona, sai nace masa gidan mu babu nisa daga inda nake.

"Sai ya ce mini gobe na fito da wuri, ni kuwa a raina na san babu abinda zai saka na dawo ofishin sa.

"Da misalin karfe 9 na safe sai naga kiranshi, yake tambayata menene yasa ban fita ba, sai na gaya mishi mahaifiyata ce ta kirani, ta ce naje Legas na kula da gida ita za ta je Dubai saro kaya.

"Tun daga wannan lokacin bai kara kirana a waya ba," in ji budurwar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel