Ina bukatar biliyan N30 duk shekara a ma'aikatar da nake jagoranta - Ministan Buhari

Ina bukatar biliyan N30 duk shekara a ma'aikatar da nake jagoranta - Ministan Buhari

Ministan shari'a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya (AGF), Abubakar Malami (SAN), ya bayyana cewa bashin da ake bin gwamnatin tarayya a ma'aikatar shari'a da yake jagoranta ya kai biliyan N150.

Ministan ya bayyana haka ne yayin da ya bayyana a gaban kwamitin majalisar dattijai a kan harkokin shari'a da kare hakkin bil'adama.

Ya ce bashin ya taru ne sakamakon rashin samun isassun kudade da zasu bawa ma'aikatar damar sauke nauyin dawainiyar da ke rataye a wuyanta.

Malami ya roki kwamitin majalisar dattijan da ya mika bukatar neman ware wa ma'aikatar shari'a biliyan N30 kowacce shekara domin ta biya basukan da ke kanta.

"Alhakin ma'aikatar shari'a ne ta biya basukan harkokin shari'a da suka rataya a wuyan gwamnatin tarayya, matsalar bashi tana matukar damun ma'aikatar shari'a.

DUBA WANNAN: Ba laifi bane ka yi 'amai ka lashe' - Sule Lamido ya fada wa su Kwankwaso

"Yawan bashin ya yi tashin gwauron zabi ne saboda tun biliyan N10 da aka taba ware wa ma'aikatar don biyan bashi a shekarar 2017, ba a kare ware wasu kudaden ba domin cigaba da biyan bashin.

"Yanzu haka yawan kudaden bashi da ake bin ma'aikatar sun haura biliyan N150, lamarin da yasa ma'aikatar ke fuskantar matsin lamba da wurin wadanda ke bin bashin,"

"Masu girma mambobin wannan kwamiti, bisa la'akari da wannan kalubalen da ma'aikatar shari'a ke fuskanta, ina neman ku saka baki domin ake ware wa ma'aikatar shari'a biliyan N30 kowacce shekara domin ta samu sukunin sauke nauyin bashin da ake bin ta,” a cewar Malami.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel