Yanzu-yanzu: FG ta bada umurnin biyan ma'aikata karin mafi karancin albashi daga watan Afrilu zuwa yau

Yanzu-yanzu: FG ta bada umurnin biyan ma'aikata karin mafi karancin albashi daga watan Afrilu zuwa yau

Majalisar zantarwan tarayya ta bada daman biyan ma'aikatan gwamnati tarayya abinda ya hau na mafi karancin albashi daga ranar 18 ga Afrilu da aka rattaba hannu kan dokar zuwa yau.

Wannan labari ya bayyana bayan zaman majalisar zantarwan tarayya da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ya jagoranta ranar Laraba, 23 ga Oktoba, 2019.

Majalisar ta yi ittifakin cewa kawai a biyan ma'aikatan cikon kudin mafi karancin albashi tun daga Afrilu tunda a lokacin aka amince za'a biya.

A ranar Talata, Kungiyar kwadago ta Trade Union Congress (TUC) ta yi kira ga gwamnatin tarayya akan ta biya bashin karancin albashi na watanni biyar a lokacin da za ta fara biya a wannan watan.

Kungiyar kwadagon wacce ta kasance daga cikin wadanda suka tattauna cikakken aiwatar da sabon karancin albashin a fadin dukkanin matakai tace tana so a biya karancin albashin tun daga lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu a dokar sabon albashin a ranar 18 ga watan Afrilu.

A ranar Alhamis, 17 ga watan Oktoba, Gwamnatin tarayya da kungiyar kwadago sun cimma matsaya kan wasu gyare-gyare a game da batun sabon albashi mafi karanci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel