Alkalai mutane ne kamar kowa, saboda haka za su iya yin kuskure – Jastis Tanko

Alkalai mutane ne kamar kowa, saboda haka za su iya yin kuskure – Jastis Tanko

Alkalin alkalan Najeriya, Jastis Ibrahim Muhammad Tanko ya ce alakalan kotun koli muatne ne kamar kowa, saboda haka za su iya aikata kuskure kamar kowa.

Daraktan yada labarai na kotun koli, Festusa Akande ne ya fitar da wannan labarin game da abinda alkalin alkalan ya fadi.

KU KARANTA:Da zafinsa: Yarinyar da ta kona kanta a kan a hanata auren saurayinta a Zamfara ta rasu

Akande ya ce Alkalin alkalan yayi wannan maganar ne a lokacin da yake karabar bakuncin hukumar kula da kadarori ta AMCON wadda ta kawo masa ziyara a ofishinsa.

“Game da yadda muke gudanar da aikinmu idan a cikinku akwai wanda yake da wani korafi to ya aiko mana da shi a rubuce.

“Ba zai taba yiwuwa ba mu ce mun san komi, saboda har yanzu koyo muke yi domin neman ilimi bai karewa har sai rai ya kare.

“Kofarmu a bude take ko da yaushe domin karbar gyara. Gyaran kuwa ko wane iri ne a kan aikinmu a shirye muke mu karbe shi. Har a wurin alamomin rubuta ana iya cinmu gyara.” Inji Alkalin alkalai.

Jastis Tanko ya fadawa bakin nasa cewa, a matsayinsu na alkalai ba su damuwa idan suka yi rubuta game da wani hukunci kuma aka ci su gyara.

Ya kara da cewa, daga Kotun koli har zuwa ta daukaka kara dukkanin alkalan a shirye suke da karbar gyara idan aka yi masu, saboda mutane ne kamar kowa za su iya yin kuskure a yayin gudanar da aikinsu.

https://www.premiumtimesng.com/news/more-news/359073-supreme-court-justices-are-humans-subject-to-mistakes-cjn.html

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel