Abin da zai sa mu kai labari a Bayelsa - Omo-Agege; Sylva, Oshiomhole

Abin da zai sa mu kai labari a Bayelsa - Omo-Agege; Sylva, Oshiomhole

A makon nan APC ta fara yakin neman zaben gwamna a jihar Bayelsa. APC ta soma yawon kamfe ne da karamar hukumar Ogbia watau Mahaifar tsohon shugaban kasa, Dr. Goodluck Jonathan.

A Ranar Litinin ne jam’iyyar mai adawa a jihar Bayelsa ta kaddamar da yakin neman zaben Nuwamba da za ayi. Jiga-jigan APC na kasa irin su Ovie Omo-Agege sun halarci wanna kamfen.

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ovie Omo-Agege da shugaban APC na kasa, Adams Oshiomhole, da karamin Ministan fetur, Timipre Sylva, sun halarci yawon kamfen din farkon.

Gwamnonin jam’iyyar APC akalla uku ne su ka dura jihar Bayelsa a Ranar 21 ga Watan Oktoba. Wadannan gwamnoni sun hada da Abubakar Bagudu; Simon Lalong da kuma Abdullahi Ganduje.

KU KARANTA: Shugaban Jam’iyyar APC ya na fuskantar barazana a hannun Gwamnan Edo

Sanata Ovie Omo-Agege ya fadawa gungun Magoya bayan da ke wurin yakin neman zaben cewa sun riga sun ci zabe sun gama. Omo-Agege yace za su yi nasara ne saboda gazawar PDP a jihar.

Sanatan yake cewa babu aikin da gwamnatin Seriake Dickson ta yi duk da irin kudin da ta samu a tsawon shekaru takwas. Wannan ya sa Sanatan yace ‘dan takarar APC David Lyon ya ci zabe.

Timpire Sylva ya fadawa mutanen jihar cewa APC ta kawo masu cigaba ne da habaka tsaro da hanyoyin inganta rayuwarsu. A cewarsu sace-sace da garkuwa da mutane ya cika mulkin PDP.

Oshiomhole wanda ya mikawa Lyon tutar jam’iyya ya caccaki gwamnatin PDP da tada rigima a jihar inda ya bada misali yadda aka tsige Tonye Isenah daga kujerar kakakin majalisar dokoki.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel