An gurfanar da wasu mutane 3 a gaban kotu kan zargin sace yaro dan shekara 4

An gurfanar da wasu mutane 3 a gaban kotu kan zargin sace yaro dan shekara 4

Wasu mutane uku a ranar Laraba, 23 ga watan Oktoba, sun gurfana a gaban wata kotun Majistare Ikeja bisa zargin sace wani yaro dan shekara hudu a duniya.

Yan sanda na tuhumar Blessinga John mai shekara 27; Blessing Itowowa mai shekara 25 da kuma Israel Ariyo mai shekara 32 akan wasu laifuka hudu da suka hada da hada kai, satar yaro, karban dan sata da kuma siyar da dan.

Sai dai kuma sun ki amsa tuhumar da ake yi masu.

Dan sanda mai kara, Inspekta Patrick Ebri, ya fada ma kotu cewa wadanda ake karan sun aikata laifin ne a ranar 14 ga watan Yuli, a gida mai lamba 261, Ikota Housing Estate, Ajah Lagos.

Ebri ya yi zargin cewa John ya sace yaron mai shekara hudu wanda ya kasance dan Mista da Misis Adegboyega Ifapohunda, daga gidan iyayensa.

“Itawowo ta karbi yaron daga hannun John sannan ya kai shi Akwa-Ibom, inda za a siyar dashi akan N350,000.

“Itowowo da Ariyo wadanda suka kasance masoya, sun shirya siyar da yaron ga wata a Akwa Ibom kan kudi N250,000."

Laifin a cewarsa ya yi karo da sashi na 277(a)(b) da 411 na dokar jihar Lagas, 2015.

Mai shari’a O.O. Fajana ta yarda da bayar da belin wadanda ake kara kan N100,000 kowannen su tare da wadanda za su tsaya masu mutum bibbiyu.

KU KARANTA KUMA: Osinbajo ya jagoranci zaman majalisar zartarwa yayinda Buhari ya halarci taro a Rasha

Ta kuma yi umurnin cewa ya zama dole wadanda za su tsaya masu su kawo takardar tabbacin biyan haaji ga gwamnatin jihar Lagas a shekaru uku da suka gabata.

Fajana ta dage shari’an zuwa ranar 18 ga watan Nuwamba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel