Ba a ga maciji tsakanin ‘Ya ‘yan Jam’iyyar APC a Jihar Edo

Ba a ga maciji tsakanin ‘Ya ‘yan Jam’iyyar APC a Jihar Edo

Daily Trust ta rahoto cewa wani sabon dar-dar ya na neman barkewa a tafiyar jam’iyyar APC mai mulki a jihar Edo yayin da ake fara shirin zaben gwamnan da za ayi a shekarar 2020 mai zuwa.

Jam’iyyar APC ta fara samun shakku ne bayan da baraka ta shiga tsakanin manyan ‘ya ‘yan jam’iyya. Hukumar NAN ta rahoto cewa wasu jiga-jigan APC ba su magana da juna a halin yanzu.

Wani Jagoran APC a jihar Edo, Janar Charles Airhiavbere mai ritaya ya fara jawo hankalin jama’a game da halin da ake ciki inda yace rigima ta yi kamari a lokacin da ya yi hira da ‘yan jarida.

Charles Airhiavbere ya bayyanawa Manema labarai cewa ‘ya ‘yan APC a jihar Edo su na fuskantar barazana wanda ka iya jefa jam’iyyar cikin matsala a zaben gwamnan da za ayi a farkon 2020.

Janar Airhiavbere yace ana kai wa shugabannin APC da ke jihar Edo hari har gidajensu. Tsohon Sojan yace wannan hare-hare na iya sa APC ta rasa zaben gwamnan da ta ke hari a shekarar badi.

KU KARANTA: Jami’an INEC sun fara hararo shirin rigima a zaben Jihar Kogi

“Mu na tir da wannan mummunan aiki. Ainihin shugabannin APC na jihar Edo ba za su yarda da wannan ba. Mu na so mu yi amfani da wannan dama mu yi Allah-wadai da harin da aka kai wa shugaban jam’iyyar APC na kasa, Kwamred Adams Oshiomhole.” Inji Janar Airhiavbere.

Airhiavbere wanda ya yi takarar tikitin gwamna a 2016 yace gwamna mai-ci da mataimakinsa da kuma SSG ne su ka sa ‘yan daba su ka kai wa Adams Oshiomhole hari domin ganin bayansa.

“Yau mutane uku sun rantse sai sun sauke Adams Oshiomhole daga kujerar shugaban jam’iyya na kasa. Bari in fada maku, ba za mu bari a ci mutuncin Oshiomhole ba. Inji Janar Airhiavbere.

Jigon na APC ya kira sunayen Mai girma Godwin Obaseki da mataimakinsa Philip Shaibu da kuma Sakataren gwamnatin jihar Edo watau Osarodion Ogie da kokarin ganin bayan Oshiomhole.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel