Hukumar INEC ta tsayar da ranar gudanar da zaben raba gardama a Katsina

Hukumar INEC ta tsayar da ranar gudanar da zaben raba gardama a Katsina

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta tsayar da ranat 30 ga watan Nuwamba domin sake gudanar da zaben kujerar dan majalisar dokokin jihar Katsina mai wakiltar mazabar Sabuwa.

Kwamishinan hukumar INEC a jihar, Alhaji Ibrahim Zarewa, shine ya sanar da hakan ranar Laraba yayin wani taro da manema labarai a Katsina.

"Za a sake gudanar da zaben ne sakamakon mutuwar tsohon dan majalisar, Ahaji Mustapha Abdullahi, wanda ya rasu sakamakon wani hatsarin mota da ya ritsa da a kan hanyar Funtua zuwa Zaria a cikin watan Yuli," a cewarsa.

Ya ce INEC ta umarci jam'iyyun siyasa su gudanar da zabukan cikin gida domin fidda 'yan takara nan da zuwa ranar 24 ga watan Oktoba.

Zarewa ya kara da cewa INEC ta tsayar da ranar 8 ga watan Nuwamba domin dawo mata da fom din CF 001, wanda 'yan takara suke cike wa.

DUBA WANNAN: Waka a bakin mai ita: Kwankwaso ya fadi su waye suka kai wa tawagarsa hari a Kano

Sannan ya kara da cewa INEC ta tsayar da ranar 18 ga watan Nuwamba a matsayin ranar da jam'iyyu zasu mika sunayen 'y'ayan jam'iyya da zasu wakilce su yayin zabe.

A cewar Zarewa, hukumar INEc ta yi wa mutane 63,135 rijista a mazabar, tare da bayyana cewa mutane 61,991 sun karbi katinsu na zabe a mazabar, yayin da ragowar katin zabe 1,142 suna ofishin INEC.

Ya ce wadanda basu karbi katin zabensu ba, suna da damar yin hakan kafin ranar da za a sake gudanar da zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel