Asirin wasu jami'an hukumar FRSC ya tonu, bayan an gawo gawar wani mutumi da suka kashe suka binne gawar shi

Asirin wasu jami'an hukumar FRSC ya tonu, bayan an gawo gawar wani mutumi da suka kashe suka binne gawar shi

- Asirin wasu jami'an hukumar kiyaye hadura ta kasa ya tonu, bayan an kama su da laifin kisan kai

- An kama jami'an 'yan sandan guda hudu da laifin kashe wani mutumi suka kuma binne gawar shi a cikin daji

- Yanzu haka dai biyu daga cikin jami'an da ake zargin sun shiga hannu, yayin da ake farautar sauran guda biyun

An tono gawar wani mutumi mai suna Odion Omafo Samuel, mai shekaru 36, wanda ake zargin wasu jami'an hukumar kiyaye hadura ta kasa (FRSC) ne guda hudu suka kashe shi suka binne.

An bayyana sunayen jami'an hukumar kiyaye haduran da Francis Igboh, Sunday Ogi, Samson Alolade da kuma Joseph Onolade.

A jiya ne rundunar 'yan sandan jihar Edo ta kama biyu daga cikin jami'an 'yan sandan da ake zargin da laifin kashe Odion akan babbar hanyar Agbor dake Benin. Biyu daga cikin jami'an da aka kama sun hada da Francis Igboh da kuma Samson Alolade inda yanzu haka suke ofishin 'yan sanda, sannan kuma jami'an 'yan sandan sun bazama neman masu laifin da suka rage.

Shaidun da aka samu bayan gabatar da bincike sun nuna cewa tsananin duka ne ya sanya Odion mutuwa, wanda kuma jami'an hukumar kiyaye haduran ne suka yi masa wannan duka saboda ya cewa direban motarsa kada ya sake ya basu cin hanci.

KU KARANTA: Tirkashi: Rikici ya barke yayin da matar fasto ta gano cewa yayi sabuwar amarya ba tare da ya sanar da ita ba

An bayyana cewa direban motar Odion din ya gudu ne da yaga abin yafi karfin shi, inda su kuma jami'an hukumar kiyaye haduran suka yi ta faman dukan shi, an garzaya da shi zuwa asibiti, sai dai da zuwan su likitoci suka tabbatar da rasuwar shi. Jami'an hukumar kiyaye haduran sun dawo dashi cikin daji suka binne shi suka gudu.

Guduwar da direban yayi ashe ya nufi kauyen su marigayin ne inda ya sanar da 'yan uwanshi halin da ake ciki, sai dai kuma sun zarge shi da cewa yayi garkuwa da dan uwan nasu ne, inda suka mika shi wajen hukumar 'yan sanda.

Bayan ya bayyanawa jami'an 'yan sandan yadda lamarin ya faru suka fara bincike akan lamarin har suka samu nasarar kama biyu daga cikinsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel