Ku tsaya a matsayin da aka sanku a zaben 2023, Jega ya roki INEC

Ku tsaya a matsayin da aka sanku a zaben 2023, Jega ya roki INEC

Tsohon shugaban hukumar INEC, Farfesa Attahiru Jega ya roki hukumar zaben mai zaman kanta da ta cigaba da zama matsayinta na ta hukumar dake cin gashin kanta a zaben shekarar 2023.

Toshon shugaban nan INEC ya ce irin wannan matsayin da hukumar take da shi ne ya sanya sauran kasahen Afirka ke kishi da ita.

KU KARANTA:Ezra Suwanta Zako: Mutum mafi tsawo a jihar Kaduna (Hotuna)

Attahiru Jega ya yi wannan maganar ne a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a wurin taron cikar dimokuradiyya shekaru 20 a Najeriya wanda Tell Magazine ta shirya.

Ana cigaba da gudanar da wannan taron a Shehu ‘Yar Adua Centre dake Abuja, a daidai lokacin da muke kawo maku wannan labarin. Taken taron kuwa shi ne ‘Dimokuradiyya da doka’.

Har ila yau, Farfesan ya yi magana a kan yadda lambar masu jefa kuri’a ke cigaba da raguwa tun daga shekarar 1999 zuwa yanzu.

Ya kara da gargadin cewa, raguwar za ta iya karuwa a zaben 2023 idan har ba a dauki matakin gaggawa ba a kan irin wannan matsala.

Haka zalika, ya yi kira ga bukatar ilharin hukumar ta dukufa wurin ganin an inganta ayyukan INEC, kasancewar akwai babban kalubale a gabanta.

A wani labarin kuwa za ku ji cewa, an samu wani matashi mai shekaru a 26 a Kaudna wanda ya fi kowa tsawo a jihar.

Sunan wannan matashin dai, Ezra Suwanta Zako wanda yake zaune a kauyen Dusai wadda ke tsakanin Kagoro da Manchock. Saboda tsanin tsawon da Allah ya zuba masa na kafa bakwai sai mutane suke kiransa dogo.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel