EFCC ta fidda sunayen 'yan damfara 10 da ta cafke a Ilorin

EFCC ta fidda sunayen 'yan damfara 10 da ta cafke a Ilorin

Jami'an hukumar EFCC mai yaki da rashawa a Najeriya, sun samu nasarar cafke wasu madamfaran yanar gizo 10 a birnin Ilorin na jihar Kwara da ke Arewacin Najeriya.

Sanarwar hakan ta fito ne faga bakin kakakin reshen hukumar, Wilson Uwujaren, yayin ganawa da manema labarai kamar yadda jaridar PM News ta ruwaito.

Hukumar mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati, ta samu nasarar cafke ababen zargin 10 a yayin wani simame da jami'anta suka kai wata maboyar 'yan damfaran dake yankin Basin na birnin Ilorin a ranar Litinin 21 ga watan Oktoba na 2019.

Mazambatan goma da suka shiga hannu a makon da muke ciki sun hadar da; Paul Chibuzor, David Daniels, Tolu Ogundowole, Tosin Ogundowole, Agwu Goodness, Olayiwola Azeez, Olamide Ijisesan, Chilaka Dickson, Abdullahi Abubakar, da kuma Temitope Bambo.

Sauran ababen da hukumar EFCC ta samu a hannun masu laifin sun hadar da wayoyin salula dama, na'aurorin kwamfuta mai tafi da gidanka, motoci na alfarma samfuri daban-daban, kudaden bogi da sauransu.

KARANTA KUMA: Yadda yawan amfani da shafukan sada zumunta ke hana bacci - Bincike

An iya tuna cewa, makkonin kadan da suka gabata hukumar EFCC a reshenta da ke birnin Ilorin na jihar Kwara, ta cafke Stephen Odanye, Abolarin Kayode, Babatunde Muhammad, Adepoju Tomiwa da kuma Akinbamidele Femi, wadanda ake zargi da aikata laifuka na zamba ta yanar gizo.

A yayin da hukumar a yanzu ta dukufa wajen gudanar da bincike, ta ce za ta gurfanar da ababen zargin a gaban Kuliya inda kowannensu zai fuskanci hukunci kwatankwancin laifin da ya aikata.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel