Yadda yawan amfani da shafukan sada zumunta ke hana bacci - Bincike

Yadda yawan amfani da shafukan sada zumunta ke hana bacci - Bincike

A wani sabon bincike da aka gudanar a kasar Birtaniya, ya nuna cewa akwai yiwuwar matasan da ke kwashe fiye da sa'o'i uku a rana suna shagaltuwa da shafukan sada zumunta, ba sa samun damar kwanciyar bacci hai sai bayan karfe sha daya na dare.

Haka kuma binciken kamar yadda jaridar BBC Hausa ta wassafa ya bayyana cewa, matasan na iya farkawa cikin dare domin ci gaba da amfani da shafukan sada zumunta.

Binciken ya kuma tabbatar da cewa, hakan na shafar matashi daya cikin uku yayin da duk wani matashi daya cikin biyar ke shafe tsawon sa'o'i biyar ko fiye da hakan a manhajojin zaurukan sada zumunta kamar su Facebook, Instagram da WhatsApp a kowace rana.

Masu binciken na jami'ar Glasgow, sun yi hasashen cewa akwai yiwuwar matasa 'yan shekara 13 zuwa 15 na jinkirin kwanciya bacci sanadiyar amfani da shafukan sada zumunta a wayoyinsu.

Likitocin lafiyar kwakwalwa wato Neurologists a Turance, sun fidda shawarar cewa ya kamata a rinka daina amfani da waya sa'a daya gabanin kwanciyar bacci.

A binciken da aka gudanar kan matasa 12,000, ya gano cewa, haramtawa matasa amfani da waya ka iya haddasa babbar matsala, domin kuwa lokci ne da suke samun damar cin gashin kansu, kuma lokaci ne mia muhimmanci da ke sadar da zumunci a tsakaninsu da abokanai.

Bugu da kari binciken ya yi hasashen cewa, lokutan da matasa ke batarwa wajen amfani da zaurukan sada zumunta na takaita lokutan da suke dauka yayin bacci.

KARANTA KUMA: Gidauniyar Dangote ta tallafawa Mata 24,000 a jihar Sakkwato

Shakka babu masana da kuma kwararrun kiwon lafiya sun tabbatar da cewa, rashin isasshen bacci na tasiri a kan lafiyar kwakwalwa da kuma yadda aikinta zai sauya ta fuskar basira.

Wata kwararra a fannin nazarin ilimin halayyar dan Adam a jami'ar Glasgow ta kasar Birtaniya, Dakta Holly Scott, ta ce duk da cewa binciken bai iya tabbatar da cewa amfani da shafukan sada zumunta na haddasa rashin isasshen bacci, sai dai tabbas yana matukar takara da baccin.

"Matasa na iya kwanciya amma idonsu biyu saboda basu shirya yin baccin ba kuma suna fargabar cewa idan suka yi bacci suka fita daga shafukan za a yi ba su"

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel