Muradin inganta jin dadin rayuwar al'umma ya sanya harkokin kasuwanci na ke ci gaba da habaka - Dangote

Muradin inganta jin dadin rayuwar al'umma ya sanya harkokin kasuwanci na ke ci gaba da habaka - Dangote

Hamshakin attajirin nan mai gidauniyar Dangote, Alhaji Aliko Dangote, na daya daga cikin mutane masu zuciyar kyauta da jin kan al'umma, lamarin da ya ce muradin inganta jin dadin rayuwarsu ta sanya harkokin kasuwancinsa ke ci gaba da habaka.

Fitaccen attajirin wanda harkokinsa na kasuwanci ke zuwa da sabbin tsare-tsaren yin sakayyar alheri ga abokanan huldarsa na ciniki, ya ce yana matukar samun kwanciyar hankali gami da farin ciki a sanadiyar inganta jin dadin rayuwar al'umma gwargwadom karfinsa.

Furucin hakan ya fito ne daga bakin daraktan cinikayya a kamfanin siminti na Dangote, Yemi Fajobi, yayin wani bikin cin gasar kyaututtuka da kamfanin ya shirya wa abokanan kasuwancinsa a birnin Akuren jihar Ondo.

A yayin da gidauniyar Dangote ke samar da kudaden shiga na kimanin naira biliyan 30, ya bayyana damuwa a kan yadda masana'antu suka gaza inganta tattalin arziki a kasar.

Dangote ya nemi al'ummar Najeriya a kan kada su debe tsammani ko kuma fidda rai da samu rabo, inda ya jaddada kudirinsa na ci gaba da bayar da tallafi domin rage radadin talauci da kuma kara yalwar arziki ta hanyar fadada harkokin kasuwancinsa da zuba hannayen jari.

KARANTA KUMA: 'Bacewar Dadiyata alama ce ta babu adalci a Najeriya - CSO

Ana iya tuna cewa, makonni kadan da suka gabata ne Dangote da ya bayar da gudunmawar dalar Amurka miliyan 20 ga wata cibiyar Afrika da ke kasar Amurka.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa, cibiyar ita ce a kan gaba wajen mayar da hankali a kan jibintar al'amuran da suka shafi Afrika da gyara suna da tarihin nahiyar a idon duniya.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel