Jami'an SARS sun samu N10m, bindigu 8 a hannun masu garkuwa da mutane a Sokoto, hotuna

Jami'an SARS sun samu N10m, bindigu 8 a hannun masu garkuwa da mutane a Sokoto, hotuna

Jami'an rundunar a jihar Sokoto sun samu zunzurutun kudi da yawansu ya kai miliyan goma da manyan bindigu kirar AK47 guda 8 a hannun wasu masu garkuwa da mutane da suka sace Alhaji Tukur Zubairu, attajirin dan kasuwa a Sokoto.

Da yake gabatar da jawabi ga manema labarai yayin bajakolin masu laifin a hedikwatar rundunar 'yan sanda masu yaki da aikata fashi da makami (SARS) da ke Abuja, kakakin rundunar 'yan sanda ta kasa, DCP Frank Mba, ya ce, "masu laifin sun hada tawagar aikata ta'addanci a lokacin da suka hadu a gidan yari a Katsina."

A cewar Mba, rundunar 'yan sanda ta kama jimillar masu laifi 81 a sassan Najeriya daban-daban, inda aka samu manyan bindigu kirar AK47 guda 8, carbin alburusai 344, na'ura mai kwakwalwa guda 1o da sauran wasu makamai na gida guda 15.

"Mun hadu a nan ne domin yi muku jawabi a kan kokarin da rundunar 'yan sanda ke yi wajen tabbatar da tsaro, kamar yadda muka dauki alkawarin gudanar da harkokinmu a bude, ba tare da rufe wani abu ba. Jami'an mu sun yi nasarar kama mambobin wata kungiyar 'yan ta'adda mai hatsari da wani mai suna Rufai ke jagoranta.

DUBA WANNAN: Badakala da almundahana: ICPC ta sanar da neman tsohon hadimin Buhari 'ruwa a jallo'

"Sun hada wannan tawaga ne a gidan yari na Katsina inda aka tsare su sakamakon aikata laifuka daban-daban kafin a yanke musu hukunci.

"Babu wanda ya san yadda suka yi suka hada kansu yayin da suke gidan yari, tun a gidan yarin suka kitsa sace Alhaji Tukur Zubairu, attajirin dan kasuw a jihar Sokoto," a cewar Mba.

Jami'an SARS sun samu N10m, bindigu 8 a hannun masu garkuwa da mutane a Sokoto, hotuna
Masu laifin da rundunar 'yan sanda ta kama
Asali: Twitter

Jami'an SARS sun samu N10m, bindigu 8 a hannun masu garkuwa da mutane a Sokoto, hotuna
Miliyan goma da aka samu a wurin masu garkuwa da mutane a Sokoto
Asali: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel