Rayuka 7 sun salwanta sannan anyi kone-konen gidaje sakamakon rikici da ya barke a Cross River

Rayuka 7 sun salwanta sannan anyi kone-konen gidaje sakamakon rikici da ya barke a Cross River

Rahotanni sun kawo cewa akalla mutane bakwai ne suka rasa ransu sakamakon barkewar wani rikicin yan kungiyar asiri a kauyen Okundi, karamar hukumar Boki, jihar Cross River.

Jaridar The Sun ta ruwaito cewa rikicin ya afku ne tsakanin mambobin garin da wata kungiyar yan asiri.

Rikicin ya afku ne sakamakon wani ganawa da mazauna kauyen suka yyi wanda aka ce suna neman hanyoyin haramta kungiyar asiri a garin.

Don haka sai kungiyar asirin da ba a ambaci sunanta ba, ta samu labarin yunkurin yan kauyen sannan ta kai wani mummunan hari akan su. An tattaro cewa dan kauyen da suka fara kashewa shine Bukie Bankong.

Wannan yunkuri na yan kungiyar asirin ya tursasa mazauna kauyen kaddamar da ramuwar gayya wanda yayi sanadiyar kashe wasu daga cikin yan kungiyar, ciki harda Joseph Bukie Bankong, Alphonsus Etta Ewung, Otu Agbor Edum, da sauransu.

KU KARANTA KUMA: Ba zai yiwu ku fadi wani mummunan abu game da Buhari ko ku zage shi ba – Sanata Gaya ga yan Najeriya

An tattaro cewa arangaman yayi sanadiyar rasa gidaje da dama da kuma dukiyoyi na miliyoyin naira.

Da yake tabbatar da harin, kwamishinan yan sandan jihar Cross River, Austine Agbnlahor, yace an tura yan sanda garin domin dawo da zaman lafiya da kuma hana cigaban hare-haren.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu

Asali: Legit.ng

Online view pixel