A karon farko: Wani babban dan adawan gwamnati ya jinjina ma namijin kokarin Buhari

A karon farko: Wani babban dan adawan gwamnati ya jinjina ma namijin kokarin Buhari

A wani yanayi da za’a iya bayyana shi da ‘basabamba’ an jiyo babban dan adawan gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Dakta Junaidu Muhammadu yana jinjina ma gwamnatin Buhari bisa wani muhimmin kokari da yake yi.

Sashin Hausa na BBC ya ruwaito Junaidu ya jinjina ma gwamnatin Buharin ne bisa kokarin da take yi musamman ta fuskar yaki da cin hanci da rashawa, inda yace babu shakka gwamnatin Buhari na kokari.

KU KARANTA: Dubu ta cika: Sojoji sun yi ram da wani mai cinikin makamai a Kaduna, sun kama AK 47 guda 6

Junaid ya yi wannan magana ne dangane da gayyatar da gwamnatin kasar Rasha ta baiwa Najeriya domin halartar taron kasashen nahiyar Afirka da kasar Rasha wanda a yanzu haka gudana a birnin Sochi na kasar.

“Kwarjinin Najeriya ya karu, kuma mutane dayawa suna ganin kasar tana da mutunci a idon duniya domin da wasan baka ake yi, ana fadan za’a yi yaki da cin hanci da rashawa amma bashi ake ba, amma wannan karon ana kokartawa, abinda ya kamata mu tayasu da addu’a Allah Ya taimakesu, domin idan yaki da hanci da rashawa ya dakushe kasar nan za ta wargaje.” Inji shi.

Najeriya dai na ci gaba da farfadowa bayan koma-bayan tattalin arzikin da ta fuskanta a 2016, kuma a yanzu haka ta rufe iyakokinta da kasashen dake makwabtaka da ita na tudu saboda matsalolin da ta ta'allak'a kan karuwar fasa-kwaurin kayayyaki.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel